Yadda aka Hana Mikawa El Rufa'i Abinci da Ganin Likita a Hannun ICPC
- Matar tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, Aisha El-Rufai, ta nuna damuwa kan cewa hukumar ICPC ta hana mika masa abinci
- Biyo bayan bayanin da ta yi a kusa da ofishin hukumar ICPC da ke Abuja, Bello El-Rufa'i ya fitar da sanarwa a madadin iyalan tsohon gwamnan
- A bayanin da Bello ya yi, ya sanar da cewa an hana mika wa Nasir El-Rufa'i abinci da ganin likita duk da cewa kotu bata hana a masa hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun zargi hukumar ICPC da tauye hakkokinsa na kundin tsarin mulki ta hanyar hana shi samun kulawar lafiya tare da takaita kai masa abinci yayin da yake tsare.
Hakan na zuwa ne bayan bayanin da matar tsohon gwamnan ta yi na cewa jami'an hukumar sun hana ta ta mika masa abincin dare.

Source: Facebook
An hana El-Rufa'i ganin likita
A cikin wata sanarwa da Bello El-Rufa'i ya wallafa a Facebook, iyalan sun ce Malam El-Rufai bai samu ganawa da likita ba duk da umarnin kotu da ya ba shi damar samun cikakkiyar damar ganin likitocinsa.
Sai dai da ya nemi ganawa da jami'in lafiya, sun ce jami’an hukumar sun hana likitan ganin sa, suna masu cewa dole sai an samu rubutaccen izini daga shugaban ICPC.
Iyalan sun bayyana matakin a matsayin karya umarnin kotu kai tsaye da kuma take hakkokin Nasir El-Rufai da doka ta tanada.
An hana El-Rufa'i karbar abinci
Sanarwar ta kuma yi zargin cewa matar El-Rufai, Asha, ita ma an kore ta lokacin da ta isa wajen da misalin ƙarfe 7:00 na yamma dauke da abincinsa na dare.
A cewar iyalan, jami’an ICPC sun gaya mata cewa ba a yarda da kawo abinci bayan ƙarfe 6:30 na yamma ba, suna danganta hakan da wasu umarnin cikin gida.

Kara karanta wannan
Malami ya yi abin kunya, kotu ta kama shi da laifin dirka wa 'yan mata ciki a Kwara
Sun yi Allah-wadai da takunkumin, suna masu cewa:
“Babu wata doka da za ta halasta hana samun kulawar lafiya ko haduwa da iyali bisa wasu dokoki na son rai.”

Source: Facebook
Iyalan sun kara da cewa:
“Ba za mu ci gaba da amincewa da wannan salon tsoratarwa da ake yi da sunan tsare wa ba. Dole ICPC ta bi dokokin da take ikirarin aiwatarwa,”
Ga bidiyon matar El-Rufa'i da the Cable ta wallafa a X:
Atiku ya nemi a saki El-Rufa'i
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta saki Malam Nasiru El-Rufai.
A sakon da ya fitar, Atiku ya bukaci sakin El-Rufa'i domin ya samu damar gudanar da bikin sallar layya a cikin iyalan shi kamar yadda kowane magidanci zai so.
Kiran Atiku Abubakar na zuwa ne duk da hukumomi ba su ba El-Rufai beli ba, lamarin da ake ganin kamar da wahala ya samu karbuwa a wajen gwamnati.
Asali: Legit.ng
