Amurka Ta Magantu kan Neman Taimakon China a Yaƙi da Iran, an Ji Abin da Suka Tattauna
- Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi magana kan ragoton cewa kasar na neman taimakon kasar China a yaki
- Rubio ya bayyana abubuwan da aka tattauna yayin ganawa da China musamman kan batun mashigar Hormuz da ake ta tababa a kai
- Ya bayyana cewa Amurka da China sun amince da hana Iran mallakar makamin nukiliya tare da kin amfani da karfin soja a mashigar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa an yada karya kan batun ganawar kasar da China.
Rubio ya tabbatar da cewa kasar ba ta bukatar taimakon China kan batun Iran duk da tattaunawar shugabannin kasashen biyu.

Source: Getty Images
China: Trump ya yi magana kan mashigar Hormuz
Rubio ya shaida wa NBC cewa Shugaba Donald Trump da shugaban China Xi Jinping sun samu fahimtar juna kan mashigar Hormuz da batun nukiliyar Iran.

Kara karanta wannan
Malami ya yi abin kunya, kotu ta kama shi da laifin dirka wa 'yan mata ciki a Kwara
Ya ce bangaren China ya bayyana rashin goyon bayansa ga militar da mashigar Hormuz tare da kin amincewa da tsarin karbar kudin wucewa a yankin.
Ya ce:
“Ba ma neman taimakon China, ba ma bukatar taimakonsu."
Rubio shi ne wanda China ta kakaba masa takunkumi tun shekarar 2020 saboda sukar da yake yi kan yadda kasar ke take hakkin bil’adama.

Source: Twitter
Takunkumin da China ta kakaba wa ministan Trump
Kafin tafiyar Donald Trump, China ta nuna cewa takunkumin ba zai hana Rubio zuwa Beijing ba saboda ya shafi ayyukansa ne a matsayin sanata, ba a matsayin ministan harkokin wajen Amurka ba.
Rubio ya ce wannan matsaya ita ce manufar Amurka, yana mai cewa kasashen biyu suna adawa da Iran mallakar makaman nukiliya masu hatsari.
Ministan ya kuma gargadi Tehran kada ta yi kokarin amfani da rikicin siyasar cikin gida a Amurka wajen matsa wa Washington a tattaunawar yarjejeniya, cewar Al Jazeera.
Rubio ya sha alwashi kan yarjejejniya a yaki
Rubio ya ce Shugaba Trump ya bayyana karara cewa Iran ba za ta iya amfani da siyasar cikin gida domin tilasta wa Amurka amincewa da yarjejeniya mara kyau ba.
Babban jami’in diflomasiyyar Amurka a birnin Beijing, ya ce Donald Trump, Xi Jinping da tawagoginsu sun shafe sama da sa’o’i biyu suna tattaunawa.
Ya ce:
“Bangaren China ya ce ba ya goyon bayan mayar da mashigar ruwa ta Hormuz wajen ayyukan soja, sannan ba ya goyon bayan tsarin karbar kudin wucewa, kuma wannan ne matsayarmu,”
Yadda tsuntsu a firgita Trump a White House
An ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya firgita yayin da wani tsuntsu ya wuce ta saman shi yana tsaka da bayani a fadar White House.
Donald Trump ya dakatar da bayanin da ya ke yi, ya koma kallon sama har ya bayyana cewa ya dauka wani jirgi maras matuki aka harbo.
Hakan na zuwa ne yayin da Amurka ke takun saka da kasashen duniya da dama da suka hada da Iran, Venezuela, China da sauran wadanda ba su ga maciji.
Asali: Legit.ng
