Shugaban kasar Amurka ya ci tuntube sau uku ya fado yayin hawa jirgin sama

Shugaban kasar Amurka ya ci tuntube sau uku ya fado yayin hawa jirgin sama

- Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya ci tuntube yayin hawa jirgin sama a yau ranar Juma'a

- Lamarin faduwar tasa, ta jawo zargin inganci da kasancewar shugaban cikin koshin lafiya

- Tuni 'yan Republican suka tabbatar da zarginsu na baya cewa shugaban na fama da rashin lafiya

Shugaba Joe Biden na kasar Amurka ya yi tuntube sau uku kuma ya fadi kan matakalan jirgin Air Force One a ranar Juma'a, wanda ya haifar da alamar tambaya game da lafiyarsa, in ji jaridar The Telegraph.

Shugaban mai shekara 78 - wanda shi ne shugaban da ya fi tsufa a tarihin shugabannin Amurka - ya bayyana a wani bidiyo yana fama dakyar yayin hawa jirgin shugaban kasar.

Ya haura kusan kashi daya cikin uku na matakalan jirgin saman, kwasam ya yi tuntube, wanda tuni ya yi wuf ya kama karfen gefe daa gefen matakalan jirgin.

KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima'i

Shugaban kasar Amurka ya ci tuntube sau uku ya fado yayin hawa jirgin sama
Shugaban kasar Amurka ya ci tuntube sau uku ya fado yayin hawa jirgin sama Hoto: thetelegraph.co.uk
Asali: UGC

Ya sake takawa zuwa gaba, hakazalika ya sake yin tuntube a karo na biyu amma ya tsaya kai da fata ya rike karfen gefe da gefen matakalan ya ci gaba da haurawa.

Shugaban bai sare ba, hakanan ya sake tashi ya ci gaba da takawa a karo na uku, ya kuma faduwa warwas, ya sake mikewa ya karkade jikinsa kafin daga bisani ya samu nasarar haurawa zuwa matakalan karshe na jirgin.

Daga nan shugaban ya yi sallama ga mutanensa ya haye cikin jirgin.

Biden, wanda ya ce yana amfani da keke kirar Peloton don kiyaye lafiyarsa, sau da yawa yakan yi maganar tsere a wasanni domin nuna lafiyar jikinsa.

Sai dai, masu zagi daga jam'iyyar Republican sun dade suna ikirarin cewa shugaban yana fama rashin cikakken lafiya da karfin jiki.

"Na kan tuna dan jaridar da ya buge Trump saboda ya taba karfen gefe da gefe na matakalan jirgin sau daya," wani ya wallafa a shafinsa na Twitter yana mai hadawa tare da bidiyon faduwar Joe Biden.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga, sun kwato bindigogi da mota a Kaduna

A wani labarin daban, Birgediya-Janar Buba Marwa ya yi kira da a gudanar da gwajin shan kwayoyi ga dalibai da ‘yan siyasa, musamman wadanda ke takarar ofisoshin gwamnati a kasar, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Marwa, wanda shi ne Shugaba kuma Babban Darakta na Hukumar hana Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a wata ganawa da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a Marina.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel