Gwamnan Bauchi zai kashe N510m domin gina hanya da magudanar ruwa.
-Gwamnan Bauchi ya kai ziyar gani da ido kan wasu ayyuka da ya bayar.
-Ayyukan sun haɗa da gina titi da kuma magudanan ruwa.
-Sannan gwamnan ya kai ziyara wasu wurare a jihar da ya haɗa har da wata makarantar sakandiren gwamnati.
@Daily_nigerian ta rawaito cewa, a ranar Asabar ne Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya sanar da ba da kwangilar gina titi mai tsawon kilomita uku tare da magudanan ruwa a garin Disina wanda zai lashe naira miliyan ɗari biyar da goma.
Gwaman ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai garin da ke ƙaramar hukumar Shira.
Ya ce, manufar wannan ziyara gani da ido ya yi ta ne domin tabbatar da an yi aikin a kan lokaci.
KU KARANTA: Rana bata karya: Ganduje ya saka ranar mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano
Gwamnan ya koka kan yadda wannan gari mai daɗaɗɗen tarihi ke fama da baranar ambaliyar ruwa, inda yai nuni da cewa gidaje da yawa sun bi ruwa.
"Ana kan aikin gina titi mai kusan tsayin kilomita uku, domin muna son farfaɗo da garin," ya faɗa.
Gwaman ya yi farin ciki da yadda aikin ke tafiya tare da kuma neman masu aikin da ƙara hanzartawa kuma su cigaba da aiki ingantacce.
A yayin da yake magana, Abdulkadir Ibrahim wanda shi ne kwamishinan Ayyuka da Zirga-zirga ya faɗa cewa al'ummar na ta roƙon wannan aiki na hanya da magudanan ruwa tun tuni.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta ji kokensu da kuma cika alƙawarinsa da ya yi a lokacin zaɓe. Sannan ya tabbatar da cewa gwamnatin ta biya kaso talatin na kuɗin aiki.
Malam Ibrahim ya tabbatar da cewa nan ba da daɗewa ba za a kammala aikin, inda yake cewa:
"Wannan ne yadda ya kamata jagoranci ya kasance. Gwamnan ya zo nan ne domin gane wa kansa domin shi ba mai zama a ofishinsa ba ne yana shan shayi tare da umartarmu mu je mu yi abu kaza ba."
Karanta wannan: Yan bindiga sun kai hari garuruwa uku a Neja cikin sa’o’i biyu, sun kashe 3 da yin garkuwa da wasu da dama
"Da zarar ya ba da umarni ga na ƙasa da shi, to yakan bi su ko'ina ne domin ganin aikin da ya bayar," a cewarsa.
Hukumar Labarai ta Ƙasa ta rawaito cewa sauran wauraren da gwamnan ya ziyarta sun haɗa da: makarantar sakandiren gwamnati da ke Zaki da fadar mai martaba sarkin Katagun da kuma ginin gidaje ɗari biyu da hamsin da ke Misau a Jalam da kuma Dambam.
A wani labarin, dalibai da sauran wadanda aka suka sace daga GSC Kagara a Jihar Neja an sake su a safiyar ranar Asabar bayan amincewar jami'ai su saki mambobin 'yan bindigan su hudu, kamar yadda majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin suka shaida wa Daily Trust ranar Lahadi.
Kungiyar 'yan bindigar sun kai hari a makarantar da ke cikin Karamar Hukumar Rafi a ranar 17 ga Fabrairu inda suka yi awon gaba da dalibai 27, da malamai 3, da ma'aikata 2 da ba sa koyarwa da iyalansu mutum 9.
Bayan kwanaki ana aiki don tuntubar wadanda suka sace su da kuma tattaunawar da ta biyo baya, an sake wadanda aka sacen ga hukumar ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da misalin karfe 7 na safiyar Asabar.
Anas Dansalma Yakasai ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci ne mai aikin fassara da rahoto a Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.
Ku biyo ni @dansalmaanas
Asali: Legit.ng