UNICEF: Yin garkuwa da yara a Zamfara take hakkin yara ne
-Garkuwa da mutane na cigaba da faruwa a Arewacin Najeiya
-A yau dai aka sake sace yara daga makaranta a Talata Mafara bayan sace na Neja da aka yi
-Wataƙila wannan ne al'amari da ya ja hankalin UNICEF inda ta koka kan al'amarin
Hukumar Tallafa wa Yara ta majalisar ɗinkin duniya (UNICEF) ta yi Allah-wadai da garkuwa da yara sama da dalibai ɗari uku da aka yi a makarantar ƴan mata ta gwamnati da ke Jangebe a ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamafara.
Ta bayyana wannan al'amari wannan hari kan ɗaliban a matsayin babban cin zarafi ne ga haƙƙin yara kuma abu mummuna da yara za su gamu da shi wanda ka iya yin tasiri a rayuwarsu da ma shafar tunaninsu da walwalarsu.
KARANTA WANNAN: Jami'an tsaro sun fara sintirin ceton 'yan matan makarantar da aka sace a Zamfara
A lokacin da yake yabawa gwamnati kan ƙoƙarin da take yi, wakilin wannan hukuma a Nijeriya, Peter Hawkins, ya buƙaci masu ruwa da tsaƙi su yi ƙoƙarin samar da tsaro a makarantu.
"Ba mu ji daɗin ba na ƙara samun wani hari kan yara ƴan makaranta a Nijeriya da aka yi," a cewarsa.
"Wannan mummunan cin zarafi ne ga take haƙƙin yara ga su kansu yaran da ka iya yin tasiri sosai ka tunaninsu da walwalarsu. Mun yi Allah-wadai da wannan abu kuma muna kira da waɗannan ƴan ta'adda da su saki yaran nan da gaggawa tare da roƙon gwamnati kan ta tabbatar da an sake su cikin ƙoshin lafiya."
"Ya kamata dai yara su zama cikin nutsuwa a gida da kuma makaranta a kodayaushe ba tare da iyaye sun shiga wani zullumi ba kan lafiyar yaran nasu bayan tura su makaranta."
KARANTA WANNANl: Yanzu Yanzu: Yan mata 317 aka sace daga makarantar GGSS a Zamfara, yan sanda
"UNICEF na kan yaba wa gwamnatin Najeriya kan ƙoƙarin tabbatar da sakin su, sannan muna kira da a ayi duk mai yuwuwa wajen samar da tsaro a makarantu."
"Wannan hari yana zuwa ne fa bayan wanda aka kai irinsa a jihar Neja kan ɗalibai ƴan makaranta wanɗanda ƙiyasinsu ya kai sama da ɗari uku.
A wani labarin kuwa, Akalla dalibai 1,140 aka sace a cikin shekaru bakwai a arewacin Najeriya, idan adadin da aka ruwaito a baya-bayan nan ya zama daidai.
Da sanyin safiyar Juma'a, wasu da ake zargin 'yan fashi ne suka kai hari makarantar sakandaren' yan mata ta Gwamnati a jihar Zamfara tare da yin garkuwa da kimanin dalibai 300, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da adadin ba a hukumance.
Harin wanda ya afku a Jangebe da ke karamar hukumar Talata-Mafara, ya jefa Najeriya cikin mummunan hali na satar dalibai sama da 1,000, jaridar TheCable ta ruwaito. Read more:
Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Sannan marubuci kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.
Ku biyo ni @dansalmaanas
Asali: Legit.ng