Janathan ya samu lambar yabo ta Zaman lafiya na Afirka na shekarar 2020

Janathan ya samu lambar yabo ta Zaman lafiya na Afirka na shekarar 2020

-Tsohon shugaban Najeriya ya samu lambar yabo na zaman lafiya a Afirka

-Sanin kowa ne cewa tun bayan karɓar rashin nasara da ya yi a zaɓen na 2015 ake ta karrama shi.

-Irin wannan ƙarramawa ce dai ya ƙara samu a jiya Juma'a daga hannun wata Mujalla daga Ingila

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Goodluck Janathan ya lashe lambar yabo na Zaman Lafiya da Tsaro na shekarar 2020 wanda wata Mujalla ta ƴan Afirka da ke Ingila ta ba shi.

Tsohon shugaban dai yana ɗaya daga cikin shugabannin da a ranar Juma'ar nan aka karrama shi da wannan lambar yabo a matsayin shugaban zaman lafiya da samar da tsaro (African Peace and Security Leader) na shekarar da ta gabata saboda gudunmwarsa ga samar da tsaro a wannan yanki na Afirka.

"A yau a karo na 9 na Karrrama Shugawagabannin Afirka na Shekara, ina mai farin cikin sanar da ku cewa an karrama ni a matsayin shugaban samar da zaman lafiya da tsaro na shekarar 2020."

"Ina gode wa wannan mujalla kan jin daɗin ƴar gudunmawa da na bayar kan zaman lafiya a Afirka," Janathan ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da Fesbuk.

Shugaba Janathan ya samu lambar girma
Janathan ya samu lambar yabo ta Zaman lafiya na Afirka na shekarar 2020. Tushe labari da hoto: Premium Times
Asali: Twitter

An ba shi wannan girmamawa ne a wani buki da aka kira da; "Shugabanci na Duniya: Sake Nazari kan Muhimman Abubuwa na Cigaba a Afirka." Wannan ba shi karo na farko ba da tsohon shugaban ƙasar ke karɓar irin wannan lambar girman.

A shekarar 2015 wata ƙunguiya mai suna 'Universal Peace Federation(UPF)' ta ba shi wannan lamba ta yabo a matsayin 'Ɗan Ƙasa Mafi Ƙaunar zaman lafiya" bayan amicewa sakamkon zaɓen na 2015 da ya yi.

Tun bayan lokaci da ya yi rashinn nasara a zaɓen na 2015, Janatahan ya cigaba da zuwa ƙasashe da yankuna a matsayin mai kiran kan tabbatar da zaman lafiya. Ɗaya daga cikin su shi ne wanda Ecowas ta tura shi domin jagoranci kan tattaunawar zaman lafiya a Mali bayan juyin mulki da sojojin suka yi.

KARANTA WANNAN: IGP: helikwaftoci na shawagi domin gano inda ɗaliban makarantar Jangebe suke

Bayan wannan, tsahon shugaban ya kai irin waccan ziyara a ƙasashen Afirka a matsayin mai sa-ido ƙarƙashin Ƙungiyar Ƙasashen Rainon Ingila da Ƙyngiyar Tarayyar Afirka da Hukumar Lura da Dimokuraɗiyya ta Kasa da Kuma Hukumar Tabbatar da Ɗorewar Dimokuraɗiyya ta Afirka (EISA).

Ya kuma jagranci jakadun Ƙungiyar Tarayyar Afirka kan sa-idon zaɓen Zambique and Tanzania kwatankwacin wanda ya yi a ƙarƙashin EISA a Afirka ta Kudu.

A bangare guda, Hukumar tsaro ta fararen kaya (DSS) ta damke Salihu Tanko-Yakasai, mai magana da yawun gwamna Kano, Abdullahi Umar ganduje bayan ya ce gwamnatin APC ta gaza.

A ranar Juma'a, Tanko-Yakasai ya bayyana damuwarsa a kan labarin kwashe yara mata na makarantar sakandaren kwana da ke Jangebe a jihar Zamfara.

Bayan sa'o'i kadan da yin tsokacin a shafinsa a Twitter, an nemi Yakasai ko kasa ko sama an rasa, The Cable ta wallafa.

Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Sannan marubuci kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Online view pixel