Kasar Rasha za ta rage kashi 50% na riga-kafin allurar 'Sputnik V' da ke maganin Kwaronabairus

Kasar Rasha za ta rage kashi 50% na riga-kafin allurar 'Sputnik V' da ke maganin Kwaronabairus

-A ƙarin samar da rigakafin da duniya ke yi kan cutar Kwaronabairus, an samu wani samfurin magani daga ƙasar Rasha.

-Wannan magani mai suna putnik V ya ya samu karɓuwa kuma yana kan samu kasancewarsa allurar farko da ka fara gwadawa.

-A na dai sa ran sauke farashin da hukumomin suka yi a Rasha ya zamto an same shi a ko'ina a duniya domin a rage kamuwa da cutar.

A ranar Alhamis ne ƙasar Rasha ta rage kuɗin maganin riga-kafin Sputnik V zuwa kudinsu na 866 rumbles wanda yai daidai da dala 12 kusan rabin kuɗin farashin maganin a baya.

Allurar dai tana da sassa guda biyu wanda hakan ya sa ta zama allura mai muhimmancin gaske. Don haka dole sai gwamnati ta kula da batun farashin nata.

KARANTA WANNAN: Bayarabe musulmi bai taba mulkin Nigeria ba tun samun ƴancin kai, MURIC ta koka

Ministan kasuwanci, Denis Manturov, ya ce, "an yanke farashin ne saboda cigaba da kuma tsare wajen samar da maganin da aka yi."

Kasar Rasha za ta rage kashi 50% na riga-kafin allurar 'Sputnik V' da ke maganin Kwaronabairus
Kasar Rasha za ta rage kashi 50% na riga-kafin allurar 'Sputnik V' da ke maganin Kwaronabairus tushe: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

Haka kuma, adadin yadda ake samar da allurar ya ƙaru a Rasha wanda hakan ne dalilin da ya sa Sputnik V ya yi araha sosai.

Duka da haka, za a mori sabon farashin ne kan tsarin da aka yi a Rasha inji ministan.

Hukumomin ƙasar Rasha ne dai suka amince da maganin na Sputnik V a watan Agusta bayan kuma ya kasance magani na farko da aka fara gwadawa a duniya, duk da cewa ba a ƙarasa gwajin karo na uku ba wanda hakan ya haifar da kace-na-nace a duniya gaba ɗaya.

KARANTA WANNAN: Wadanda suka so Jonathan ya fadi zabe ne ke daukar nauyin 'yan bindiga, Mailafia

Rasha dai ta yi nasarar rijistar allurar a ƙasashen 36 kamar yadda alƙaluman Hukumar Zuba Hannun Jari ya nuna.

A bangare guda, K'ungiyar Tarayyar Afirka ta roƙi masu samar da rigafin Kwabid-19 kan su sahale hakkin mallakarsu.

"Kusan mutane miliyan sha biyu ne suka mutu, kuma wannan misali ne kawai. Sahalewar dai za ta taimaki kowa da kowa saboda babu wanda ke son kallon abu marar daɗi na cigaba da faruwa. Muna son mu zama tarihi ya yi alfahari da mu," ya faɗa.

A wani ɓangaren ma., darakta na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Matshidiso Moeti, ta yi irin wannan kira da kamfanonin samar da magunguna kan wannan haƙƙi domin a samu magunguna cikin sauƙi.

Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci, malami kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa shi ne zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng