An Cafke Dan Bindiga da Ya Je zai Karbi Miliyoyin Kudin Fansa

An Cafke Dan Bindiga da Ya Je zai Karbi Miliyoyin Kudin Fansa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta cafke wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne yayin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa na N10m
  • An sace wanda aka yi garkuwa da shi, wanda aka bayyana da suna Alhaji Bagudu daga gidansa a ƙauyen Ilowa da ke Oyo a makon da ya gabata
  • Rahotanni sun nuna cewa daga baya an tafi da shi da ƙarfi zuwa dajin Otefon, inda aka tsare shi har sai an biya kuɗin fansa da aka nema

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a daidai lokacin da yake karɓar kuɗin fansa na Naira miliyan 10.

Bayanin da 'yan sanda suka yi ya nuna cewa an kama wanda ake zargin yana shirin karbar kudi a hannun dangin wani wanda aka sace a ƙauyen Otefon, cikin ƙaramar hukumar Atiba ta jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Hankalin Wike ya tashi da gwamnan Oyo ya fito zai kara da Tinubu a 2027

Taswirar jihar Oyo
Taswirar jihar Oyo a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Punch ta rahoto cewa 'yan bindiga sun sace wanda aka yi garkuwa da shi, Alhaji Bagudu sannan aka tafi da shi dajin Otefon, inda masu garkuwar suka tsare shi tare suna neman kuɗin fansa kafin su sake shi.

Yadda aka kama dan bindiga

Da yake tabbatar da kama wanda ake zargin a ranar Alhamis, kakakin ‘yan sanda na jihar, Olayinka Ayanlade, ya yi karin bayani kan lamarin.

Ayandale ya ce sahihin bayanan sirri daga jami’an kungiyar 'yan sa-kai reshen Oyo ne ya taimaka wajen dakile karɓar kuɗin fansar.

Ya ce a ranar Laraba da misalin ƙarfe 1:00 na dare, an samu bayanai cewa wasu masu garkuwa sun taru a dajin Otefon domin karɓar kuɗin fansa daga dangin wanda aka sace.

Binciken da 'yan sanda suka yi

Binciken farko ya nuna cewa kimanin mutane shida ɗauke da makamai sun kai hari gidan Alhaji Bagudu a ranar 9 ga Mayu, 2026, suka sace shi, sannan suka tafi da shi cikin daji inda suka nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 10.

Kara karanta wannan

Mai son takarar gwamna ya yi gargadin tarwatsewar APC a Taraba

Ya bayyana cewa jami’an sun yi amfani da dabarun aiki domin tabbatar da an saki wanda aka sace cikin koshin lafiya kafin su kai farmaki kan masu laifin.

The Nation ta rahoto ya ce:

“Bayan an tabbatar cewa an saki wanda aka sace ba tare da wata matsala ba, jami’an sun tunkari wurin da aka taru domin karɓar kuɗin fansar,”

Ayanlade ya ƙara da cewa da ganin jami’an tsaro, masu laifin suka buɗe wuta, a nan aka kama ɗaya daga cikinsu mai suna Mohammed Sani, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji da raunin harbin bindiga.

Gwamna Seyi Makinde
Gwamna Seyi Makinde yayin wani taro a Ibadan. Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

An kashe sarki a Kogi

A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kashe wani sarki da suka sace a jihar Kogi mai suna Adebayo Samuel.

Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa sarkin ya shafe kwanaki a wajen 'yan ta'addan a cikin daji suna neman a biyasu kudin fansa.

Mutanen garin da Adebayo Samuel ke mulki sun cika fadarsa suna jimami game da abin da ya faru da shi, suna kira ga gwamnati ta dauki mataki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng