Ranar NGOs ta duniya: Minista Sadiya ta yabawa kungiyoyin tallafi kan ƙoƙarin da suke yi

Ranar NGOs ta duniya: Minista Sadiya ta yabawa kungiyoyin tallafi kan ƙoƙarin da suke yi

-Minista Sadiya ta bayyana farin cikinta ga yadda ƙungiyoyi masu zaman kansu ke taimakawa al'umma.

-Ranar 27 ga watan Fabarairu ne ranar da ka ware domin tunawa da irin gudunmawarsu.

-Ta yi fatan cewa za su cigaba da samun haɗin kai da hukumarta domin taimaka wa al'umma.

A ruwayar Nigerian Tribune, Ministar ba da gaji da walwalan al'umma ta yi matuƙar yaba wa ƙungiyoyi masu zaman kansu ga halin sanin yakamata da suke nunawa wajen haɗa kai da Hukumarta a yayin murnar ranar Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu na Duniya (NGOs).

KU KARANTA:'Yan bindiga sun sake komawa Kagara, sun bindige mutum hudu har lahira

A ranar 27 ga watan Fabarairun kowacce shekara, rana ce ta Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu na Duniya wanda ake yi a kusan kasashe tamanin da tara.

Ministar ta jinjinawa Ƙungiyoyin kan irin gudunmawar da suke bayarwa wanda ya sa aka ware ranar nan domin yin murna da tunawa da kuma haɗuwa da juna a duk faɗin duniya.

Minista ma'aikatar ba da agaji ta yaba wa NGOs kan irin ƙoƙarin da suke yi
Ministar ma'aikatar agaji ta yaba wa NGOs ƙoƙarin da suke yi Tushen Hoto da labari: Nigerian Tribune.
Asali: Twitter

Ministar ta waiwayi irin nasarorin da irin waɗannan ƙungiyoyi suka yi, inda take cewa:

"A yau muna murnar ranar Ƙungiyoyi na Duniya masu zaman kansu kuma abokan haɗin guiwarmu wajen inganta rayuwar al'umma musamman a lokacin da aka sha fama da annobar Kwabid-19," tace.

Sannan ta ƙara da cewa; "Muhimmancin irin waɗannan ƙungiyoyi ga cigaban muhallanmu da da ƙasa da ma duniya baki ɗaya ba zai iya faɗuwa ba."

KARANTA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dalibai da malaman Kagara da aka sako sun isa garin Minna

"Waɗannan ƙungiyoyin sa-kai sun kan ƙoƙarin inganta rayuwar na ƙasa waɗanda a alokacin wannan annoba suka riƙa ba da tallafin abinci da man wake hannu da takunkumi da sauran kayan tallafi."

"A yau muna jinjina muku tare da fatan wannan alaƙa tamu za ta ɗore wajen taimaka wa al'umma a lokuta da ake cikin tsanani," ministar ta faɗa.

A bangare guda, An saki amaryar da aka sace a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Alhamis.

An sace ta tare da kawayenta da kuma wasu mutane da ke bin hanyar a lokacin da maharan suka kai harin.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa maharan sun sauke wadanda lamarin ya rutsa da su a wani kauye kusa da Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da tsakar dare. Read more:

Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Sannan marubuci kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng