Masu Kula da majinyata a Asibiti sun tsunduma Yajin aikin gargadi a Jihar Ondo

Masu Kula da majinyata a Asibiti sun tsunduma Yajin aikin gargadi a Jihar Ondo

- A watan daya gabata ne Kungiyar likiticin jihar suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

- Ranar Alhamisa Jami'an na jinya zasu koma bakin aikin su Kamar yadda shugabansu ya fada

- Manyan jihar sun nuna takaicin su akan wannan lamari

Kungiyar Masu kula da majinyata da masu karbar haihuwa (NANNM) ta tsunguma yajin aikin gargadi na kwana uku a yau Litinin 1 March, 2021 saboda biyansu rabin Albashin su.

Yajin aikin ya tsayar da duk wani aiki na Asibitocin Jihar saboda kasancewar Likitoci ma na yajin aiki tun watan daya gabata.

A rahoton da jaridar thenation ta wallafa, an gano cewa babu wani sabon mara lafiya da aka amsa da fadin jihar sannan kuma shuwagabannin asibitoci na ta sallamar majinyata kasan cewar babu masu kula dasu.

Dukkan bangarorin kwantar da mara lafiya a asibitin koyarwa na jami'ar likitoci dake babbar birnin Jihar Akure sun kasance babu kowa sai yan kadan wadanda ba'a rigada an sallama ba.

KU KARANTA: Munguno: Muna da rahotannin sirri na wadanda ke cin gajiyar rashin tsaro

Masu Kula da majinyata a Asibiti sun tsunduma Yajin aikin gargadi a Jihar Ondo
Masu Kula da majinyata a Asibiti sun tsunduma Yajin aikin gargadi a Jihar Ondo
Asali: Instagram

DUBA NAN: Wike ya sasanta gwamnan jihar Benue da na Bauchi kan batun makiyaya

Shugaban Kungiyar NANNM reshen Jihar, Comrade Olumiye Kehinde ya bayyana cewa, yajin aikin da suka shiga na gargadi ne kuma zasu dawo bakin aiki ranar Alhamis.

Babban Darakta na UNIMEDTH, Dr. Oluwole Ige ya ayyana yajin aikin amastayin babban kaluale. Yakuma kara da cewa babu wani sabon majinyaci da aka amsa a asibitin.

Ige ya kara cewa, an riga da an shiga filin tattaunawa domin ganin dukkan ma'aikatan sun dawo bakin aikin su. Yakuma yi kira da likitoci da jami'an jinya da su nuna halin dattako domin za'a biya su sauran albashinsu.

Daga cikin kalamansa yace "Wannan babban rauni ne amma muna cigaba da tattaunawa da likitoci. Munyi taro yau kuma muna fatan anfara fahimtar Juna.

Abinda Jami'an jinya suke bukata sun hada da, biyan su dukkan albashin su na Junairun 2017, Disamban 2020, Junairu 2021, cikashen kashi 20 na albashin Disamba 2016, biyansu ragowar rabin albashin Nuwamba 2016 da kuma fara aiwatar da sabon tsarin albashin ma'aikatan jinya na kanan hukumomi tsakanin kwanaki bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel