Burutai: ƴan Najeriya sam ba sa yaba wa ƙoƙarin da sojoji ke yi na magance matsalar tsaro

Burutai: ƴan Najeriya sam ba sa yaba wa ƙoƙarin da sojoji ke yi na magance matsalar tsaro

-Tsohon shugaban rundunar sojoji ta ƙasa ya ce mutane ba sa yaba wa sojoji kwata-kwata

-Ya faɗi hakan nne dai a yayin wani taron addu'a da Oba Adekunle Oyelude ya shirya masa.

-Burtai dai ya gina musu wata gada ce da ta haɗa ƙauyuka biyu wanda tai shekaru a lalace.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon shugaban rundunar sojoji ta ƙasa, Tukur Burutai (mai ritaya), ya ce sam mutanen Najeriya ba sa yaba ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen magance matsalar tsaro a ƙasar nan.

Tsohon shugaban ya yi wannan batu ne a garin Kuta na jihar Osun a wani taron addu'a da Olowu na Kuta, Oba Adekunle Oyelude ya shirya masa a fadarsa.

Ya samu rakiya biyu daga cikin tsofafin ƴan ajinsu, manjo Daniel Banjo (mai ritaya) da kwamanda na yanki Mamman Yusuf (mai ritaya). .

Burutai ya ce sau uku ana kai masa hari a yayin yaƙi da ƴan ta'adda.

Sannan ya tabbatar wa da al'ummar yankin cewa za a cigaba da lasawa duk da kasancewar ya bar aikinsa.

Karanta wannan: Tawagar samu gyaran wutar lantarki a Borno ta ci karo da nakiyar da ISWAP suka dasa

Burutai: ƴan Najeriya sam ba sa yaba wa ƙoƙarin da sojoji ke yi na magance matsalar tsaro
Burutai: ƴan Najeriya sam ba sa yaba wa ƙoƙarin da sojoji ke yi na magance matsalar tsaro Tushe: The Punch
Asali: Twitter

"A filin daga, abubuwa da yawa na faruwa, sai dai ƴan Najeriya ba sa godewa. Sau uku ana kai min hari, a inda sai dai mu shige daji da ni da yarana, sannan muka juya mu mai da martani. Dangantakata da Olowu Allah ne ya haɗa ta," in ji Burutai.

A yayin da yake nasa maganar, Olowu na Kuta, Oba Oyelude, ya bayyana cewa al'ummar wannan yanki za su cigaba da yin godiya ga Burutai game da irin taimakon da ya ba su na ƙarasa musu gadar da ta haɗa su da garin Ede.

Oban Oyelede ya ce, "Shekaru masu da yawa, an yi ƴan siyasa manya sun yi ƙoƙarin taimakon mu wajen gina wannan gada, amma sun gagara, sai dai bayan kawo maka kukanmu ga Burutai; nan ya amsa tare da tattabatar da an kammala."

"Wannan babbar nasara ce a gare ni a matsayin sarki. Gadar ta shafe sama da shekaru, amma sai yanzu al'ummar yanki suka samu haɗuwa da ɗayan ƙauyen."

Karanta wannan: Domin ceto daliban Jangebe, Gwamnan Zamfara ya nemi taimakon Auwalu Daudawa da dan Buharin Daji

"Ina goyon bayan sojoji ne saboda Burutai domin babu ruwansa da ƙabilanci kuma mafi tausayin shugaban sojoji. Za mu iya samun zaman lafiya ne kawai idan muka mara wa sojoji baya a ƙaƙarinsu na magance matsalar tsaro ba tare da la'akari da su waye shuwagabanninta ba."

An dai yi addu'o'i ga tsohon shugaban daga bakin malamai Musulmi da kuma Kirista a yayin taron da ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen jihar ta Osun.

A wani labarin kuma: tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yabawa Salihu Tanko Yakasai, hadimin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da aka sallama saboda sukar Buhari a shafinsa na Twitter.

Fayose ya yi wannan jinjinan ne bayan Alhaji Tanko Yakasai, mahaifin Salihu Tanko Yakasai ya bada rahoton cewa jami'an tsaro sun kama dansa saboda ya ce Shugaba Buhari ya yi murabus yayin Allah wadai da sace ɗaliban GGSS Jangebe a jihar Zamfara.

Anas Dansalma Yakasai ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci ne mai aikin fassara da rahoto a Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Online view pixel