Kotu Ta Yanke wa Malamin Addinin Musulunci Daurin Rai da Rai a Birtaniya

Kotu Ta Yanke wa Malamin Addinin Musulunci Daurin Rai da Rai a Birtaniya

  • Wata kotu a Birtaniya ta yanke wa tsohon limami hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun shi da laifuffuka da dama da suka shafi cin zarafi
  • Rahotanni sun nuna cewa Abdul Halim Khan ya yi amfani da matsayinsa na limami wajen yaudarar wadanda abin ya shafa
  • Alkalin kotu ya bayyana Khan a matsayin mutum mai matukar hatsari bayan samunsa da laifuffuka 21 da suka hada da cin zarafin yara kanana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

London, UK - Wata kotu da ke kasar Birtaniya ta yanke wa tsohon limami Abdul Halim Khan hukuncin daurin rai da rai saboda fyade da cin zarafin mata da yara.

Rahotanni sun bayyana cewa Khan mai shekaru 54 ya aikata laifuffukan ne tsakanin shekarar 2004 zuwa 2015 a yankin gabashin London.

Kara karanta wannan

Malami ya yi abin kunya, kotu ta kama shi da laifin dirka wa 'yan mata ciki a Kwara

An ɗaure liman har tsawon rayuwarsa a Birtaniya
Kotun 'Crown' da ke Birtaniya, limami Abdul Halim Khan da aka ɗaure a gidan kaso. Hoto: The Independent, Joe Giddens/PA.
Source: Getty Images

An ce ya yi amfani da matsayinsa na jagoran addini wajen yaudarar mata da kananan yara domin cin zarafinsu ta hanyoyi daban-daban, cewar Sky News.

Hukuncin da kotun ta yanke wa liman

Kotun ta same shi da laifuka 21 da suka hada da cin zarafin yara ‘yan kasa da shekaru 13 da kuma wasu laifuffukan lalata.

Alkalin kotun, Leslie Cuthbert, ya bayyana cewa Khan ya yi amfani da amincewar da mutane suka ba shi wajen aikata munanan laifuka.

Kotun ta umurce shi da zaman gidan yari na akalla shekaru 20 kafin a yi la’akari da yiwuwar sake shi daga kurkuku.

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa ta bayyana Khan a matsayin “mugun mutum mai hatsari” saboda irin wahalar da ta fuskanta a hannunsa.

An tura limami a gidan yarin Birtaniya
Masallacin Umar da ke birnin Leicester a Birtaniya. (An yi amfani da hoton ne don misali kawai, ba shi da alaƙa da labarin.) Hoto: Ross Kinnaird.
Source: Getty Images

Abin da wata yarinya ta ce kan liman

Wata yarinya da aka ci zarafinta tun tana karama ta ce Khan ya yi amfani da tsoro da barazana wajen hana ta bayyana abin da ya aikata, cewar rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

Hukumar masu gabatar da kara ta ce Khan kan kai wadanda abin ya shafa wurare masu nisa kafin ya yi amfani da ikirarin aljanu wajen tsoratar da su.

An bayyana cewa dukkan wadanda aka ci zarafinsu ‘yan asalin al’ummar Musulman Bangladesh ne da ke zaune a yankin da shi limamin ya ke limanci.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya fara bayyana ne bayan daya daga cikin wadanda abin ya shafa ta kai kara ga malamarta a makaranta a 2018.

Jami’an ‘yan sanda sun yaba da jarumtar wadanda suka kai rahoto, suna mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da adalci ga wadanda aka zalunta.

Wani dauke da makami ya tarwatsa masallata

A wani labarin, kun ji cewa wani mutumi dauke da makami ya shiga babban masallacin birnin Manchester da ke kasar Birtaniya mai daukar musulmai sama da 5,000.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Talata amma tuni yan sanda suka kama shi tare da kaddamar da bincike kan lamarin

Kwamitin Masallacin ya bayyana cewa mutane biyu aka gani da alamun zargi, an kama daya amma dayan ya gudu inda ake ci gaba da nemansa har zuwa lokacin hada rahoton.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.