Kungiyar Tarayyar Afirka ta roƙi masu samar da rigafin Kwabid-19 kan sahale hakkin mallakarsu

Kungiyar Tarayyar Afirka ta roƙi masu samar da rigafin Kwabid-19 kan sahale hakkin mallakarsu

-Cutar Kwarona dai na cigaba da kama mutane a ƙasahe da yawa duk ƙoƙarin samar da magunguna da ake yi.

-Wannan dalili ne ya sa wasu ƙasahe biyu a labarin suka buƙaci a kanfanonin samar da maguungunan da su sahale haƙƙin mallakarsu.

-Haka kuma an samu magunguna na Hukumar Tantance magunguna ta Afirka ke duba su don fara amfani da su.

Jaridar The Tribune a ranar Alhamis ne dai Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta nuna goyon bayanta kan kiraye-kiraye da ake yi a kan sahale haƙƙin mallaka daga masu samar da magugunan rigakafin Kwabid-19.

Ƙungiyar ta nuna wajabtuwar kiran nata ne saboda tabbatar da an isar da magungunan ga ƙasahe marasa ƙarfi.

KARANTA WANNAN: Alkali Abdul Kafarati ya rigamu gidan gaskiya

Ƙasashen Afirka ta Kudu da Indiya na kan samar da magungunan kuma sun nuna buƙatar hakan a taron Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya.

Ƙasashen biyu dai sun nuna cewa dokar haƙƙin malakar ta (IP) na yi wa yunƙurin cikas wajen samar da magugunan da yawa ga marasa lafiya.

Sun dai gamu da rashin goyon baya daga manyan ƙasashen, amma goyon bayan Ƙungiyar Tarayyar Afirka ka iya taimakawa wajen sausauta waccan ƙa'ida.

John Nkengasong ne dai daraktan Hukumar Lura da Cuttuka da Hana Aukuwarsu ta Afirka wanda kuma ya sanar da cewa sassaucin zai ƙara samar da nasara ga duka ɓangarorin wajen magance bambanci a fannin lafiya a duniya.

Ya ba da misalai biyu na yadda ƙasashe masu tasowa suka wahala saboda iyaka da suke da shi na samun magunguna kamar lokacin annobar swine flu a shekarar 2000 da kuma na HIV/AIDS a shekarar 1990.

"A 1996, an samu maganin HIV kuma mun ga yadda aka samu ƙaracin rashe-rashe a manyan ƙasashen na duniya. amma abun zai ɗauke mu shekaru goma kafin mu iya samun kai wa ga magungunan a Afirka," a cewarsa.

K'ungiyar Tarayyar Afirka: Ta roƙi masu samar da rigafin Kwabid-19 kan sahale hakkin mallakarsu
K'ungiyar Tarayyar Afirka: Ta roƙi masu samar da rigafin Kwabid-19 kan sahale hakkin mallakarsu. Source: Nigerian Tribune
Source: Twitter

"Kusan mutane miliyan sha biyu ne suka mutu, kuma wannan misali ne kawai. Sahalewar dai za ta taimaki kowa da kowa saboda babu wanda ke son kallon abu marar daɗi na cigaba da faruwa. Muna son mu zama tarihi ya yi alfahari da mu," ya faɗa.

A wani ɓangaren ma., darakta na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Matshidiso Moeti, ta yi irin wannan kira da kamfanonin samar da magunguna kan wannan haƙƙi domin a samu magunguna cikin sauƙi.

Ta bayyana fatanta na cewa za a yi nasara kan wannan batu, "za a cimma hakan a nan gaba kaɗan," a cewarta.

Nkengasong, ya ce Hukumar ta fi da CDC ta amincce da rigakafin "AstraZeneca’s COVID-19" domin amfani na gaggawa bayan kwana ɗaya da ƙasar Ghana ta amshi nata rigakafin na AstraZeneca daga masu raba maguguna na duniya (COVAX).

A cewarsa, wata hukumar samar da maganin na Kwarona da ke Russia ta bayar da bayanai a kan maganin "Sputnik V vaccine" kuma Hukumar ta CDC ta Afirka na kan tace shi.

KARANTA WANNAN: Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan tada ƙayar baya goma sha ɗaya

"Ba mu amshi wani magani daga ƙasar Sin ba har zuwa yanzu, amma muna sa-rai," in ji shi.

Ƙasar Masar da Zimbabwe da Senegal sun riga sun fara gwada maganin na Sin.

A wani labarin kuwa, Gwamnatin jihar Zamfara ta ce bata san adadin dalibai matan da aka sace daga makarantar gwamnatin mata na GGSS Jangebe ba.

Legit Hausa ta ruwaito yadda yan bindiga suka kwashe dalibai mata daga makarantar misalin karfe daya na daren Juma'a.

Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce an sace dalibai sama da 300.

Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Sannan marubuci kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Source: Legit.ng

Online view pixel