Dangote, BUA, Tiamin sun bayyana niyyar baiwa daliban da Kwankwaso ya ba wa tallafin karatu ayyuka

Dangote, BUA, Tiamin sun bayyana niyyar baiwa daliban da Kwankwaso ya ba wa tallafin karatu ayyuka

-Kwanakin baya ne dai ɗalibai 370 suka kammala karatunsu tare da dawo wa gida Najeriya

-Ɗaliban waɗanda suka ci gajiyar gidauniyar Kwankwaso za su ƙara samun wani tagomashin

-Domin kuwa wasu kamfanoni sun yi alƙawarin ba su ayyukan yi nan ba da daɗewa ba

Jaridar Daily Nigeria ta rawaito Dangote, BUA, Tiamin Rice sun sanar da niyyarsu ta ɗaukar ɗalibai 370 da suka ci gajiyar tallafin karatu na ƙasar waje wanda tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya ba su.

An yi wannan sanarwa ne a ranar Asabar lokacin da ake taron ƙaddamar da samar da aikin yi ga ɗaliban ƙasar waje da Kwankwaso ya ba wa tallafi.

Mansur Ahmad na kanfanin Dangote da Idi Hong na kanfanin BUA and Sagir Ahmed na kanfanin Tiamin Rice sun tabbatar da cewa kowannensu zai ɗebi kasonsa domin ba su ayyuka.

KARANTA WANNAN: Ku daina baiwa yan bindiga kudi ya na da hadari, Buhari ya gargadi gwamnoni

Dangote, BUA, Tiamin Rice: Za su ba wa ɗaliban ƙasar waje da Kwankwaso ya ba wa tallafin karatu ayyuka
Dangote, BUA, Tiamin Rice: Za su ba wa ɗaliban ƙasar waje da Kwankwaso ya ba wa tallafin karatu ayyuka Tushe: @Daily_nigerian
Asali: Facebook

Sun tabbatar da cewa ɗaliban waɗanda mafi yawa ke digiri mai daraja ta ɗaya (first class) za su dace da kanfanunuwansu.

A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa, Kwankwaso ya ce ya yi farin cikin ganin ɗaliban da gidauniyarsa ta ɗau nauyi sun dawo cikin ƙoshin lafiya da kuma digirinsu na biyu a ɓangarori daban-daban.

Ya ƙara da cewa ɗaliban dai sun ci gajiya tallafi ne da ya haɗa da biya musu kuɗin makaranta, kuɗin jirgi, wurin kwana da na rayuwa ta yau da kullum a yayin da karatun nasu.

KARANTA: Janathan ya samu lambar yabo ta Zaman lafiya na Afirka na shekarar 2020

Sannan gwamnan ya bayyana cewa jami'ar ta Mewer dake Indiya ta ba wa mutane sha uku cikin ɗari uku da saba'in aikin lakcarin tare da tallafin karatun digiri na uku (PhD).

Ɗaliban dai akwai na Indiya da Sudan da Dubai, duk ƙarƙashin gidauniyar ta Kwankwasiyya.

Wasu daga cikin iyayen yaran sun yaba wa Kwankwaso kan wannan aikin alheri tare da jan hankalin ɗaiɗikun mutanen kan su yi koyi da shi.

A wani labarin dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi maraba da sakin daliban da aka sace na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara, Jihar Neja, Nigerian Tribune ta ruwaito.

A wata sanarwa da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban Kasa a kafofin watsa labarai ya fitar a ranar Asabar, ya ce Shugaban kasar ya yaba wa hukumomin tsaro da na leken asiri kasae da kuma gwamnatin jihar Neja kan martaninsu wajen ceto yaran. Read more:

Anas Dansalma Yakasai ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci ne mai aikin fassara da rahoto a Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng