Shugaban kasar Argentina ya sha ruwan duwatsu daga 'yan zanga-zanga a kasarsa
- A yayin wata zanga-zanga a kasar Argentina, shugaban kasar ya sha ruwan duwatsu ba tsammani
- Mutanen wani na Chubut a kasar sun nuna fushinsu a wata zanga-zanga tare da jifar shugaban
- An ruwaito cewa, suna zanga-zangar ne don neman sake bude wurin hakar ma'adanai a yankin
Dandazon masu zanga-zanga ne suka kai wa motar da Shugaban kasar Argentina ke ciki hari a yankin Patagonia na kasar.
Dandazon mutanen sun taru a kan motar Alberto Fernández kuma suka fara jifansa da duwatsu da dukan motar a kofar wata cibiyar mazauna yankin Chubut.
Shugaban kasar na yin ziyarar jaje ne ga mutanen da gobarar daji ta shafa, wadda ta kashe mutumdaya tare da raunata wani.
KU KARANTA: Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18
Sai dai ana gudanar da znaga-zangar ce domin neman sake bude wani wurin hakar ma'adanai a Chubut.
Mutanen na fushi da shirin gwamnatin na amincewa da manyan ayyukan da ake shirin farawa a yankin wanda ke da arzikin zinare da tagulla da uranium, a cewar rahoton jaridar Clarín, abin da ka iya kawo cikas ga harkokin hakar ma'adanan.
KU KARANTA: Mijin Zahra Buhari ya nuna hotunansa tare da zakin da yake wasa dashi a gida, ya jawo cece-kuce
A wani labarin daban, Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da kawayenta, a ranar Laraba, za su fara zanga-zanga a duk fadin kasar kan matakin da Majalisar Dokoki ta Kasa ta dauka na cire mafi karancin albashi daga jerin dokoki na musamman zuwa jerin dokokin majalisar.
Takardar gayyata a hukumance da Majalisar ta aike wa kungiyar kwadago ta bayyana cewa tattara mambobin zai fara ne daga Unity Fountain Abuja da karfe 7:30 na safe, kuma za su tafi farfajiyar Majalisar Dokoki ta kasa don nuna bacin ransu kan matakin.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng