Labaran Duniya
Yayin da ake ci gaba da musayar wuta a Gabas ta Tsakiya, Jamus ta roki China ta yi amfani da tasirinta ta lallaba Iran domin a kawo karshen wannan rikicin.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa karfin soji ba zai iya warware matsalar shirin nukiliyar Iran ko bude mashigar ruwa ta Hormuz ba.
Hedkwatar rundunar sojojin Iran ta umarci manyan hafsoshi su kara sa ido kan yiwuwar shigar da dakarun makiya cikin kasar bayan barazanar Shugaba Donald Trump.
Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya musanta abubuwan da ake yadawa game da kasar, ya bayyana cewa ba su taba tayar da yaki ba amma suka kare kansu.
Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Iran ta fito ta yi martani kan kalaman da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi na cewa tana neman tsagaita wuta.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ya jaddada goyon baya ga kungiyar Hezbolla a wata zungureriyar wasika da ya aika wa shugaban kungiyar, Nim Qassem.
Rundunar IRGC ta kasar Iran ta ƙaddamar da gagarumin harin ramuwar gayya da makamai sama da 300 kan sansanonin sojin Amurka da Isra'ila a yau Laraba.
A labarin nan, za a ji cewa rahotanni sun tabbatar da yadda ake samun karuwar rasa rayuka yayin da makaman da Iran ke harba wa ke yi wa Isra'ila illa.
Sojojin Checheniya da ke kasar Rasha sun shirya shiga yakin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Za su taimakawa kasar Iran kan yaki da Amurka.
Labaran Duniya
Samu kari