Iran Ta Fara Cin Gajiyar Kulle Mashigar Hormuz duk da Matsin Lambar Amurka

Iran Ta Fara Cin Gajiyar Kulle Mashigar Hormuz duk da Matsin Lambar Amurka

  • Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara cin gajiyar kulle mashigar ruwa ta Hormuz wadda ke da muhimmanci wajen jigilar mai da iskar gas
  • Mataimakin Majalisar dokokin Iran, Hamidreza Habibaei, ya bayyana cewa an fara biyan harajin da aka kakaba don wucewa ta mashigar
  • Hakan dai na zuwa ne duk da matsin lambar da Shugaban Amurka, Donald Trump, yake yi domin ganin Iran ta bude mashigar da ke tsakanin teku

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Wani babban jami’in majalisar dokokin Iran, Hamidreza Hajibabaei, ya bayyana cewa Tehran ta karɓi kuɗaɗen shiga a mashigar ruwa ta Hormuz.

Jami'in wanda yake da matsayin Mataimakin shugaban majalisa ya bayyana cewa an karbi kudaden shiga na farko daga harajin da Iran ta sanyawa mashigar ruwa ta Hormuz a yaƙin da take yi da Amurka da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Majalisa na shirin tsige gwamna a Najeriya, an ji yadda zancen yake

Iran ta fara samun kudade daga mashigar Hormuz
Hoton taswirar mashigar ruwa ta Hormuz Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa jami'in Majalisar dokokin ta Iran ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026.

Me Iran ta fara samu daga Hormuz?

Mataimakin shugaban majalisar dokokin ya bayyana cewa an adana kudaden shigar da aka samu a babban bankin kasar Iran.

“Kuɗaɗen shiga na farko da aka samu daga harajin mashigar Hormuz an adana su a asusun Babban Bankin ƙasa."

- Hamidreza Habibaei

Sauran kafafan yaɗa labaran Iran sun yaɗa wannan bayani na dan majalisar ba tare da yin wani dogon ƙarin bayani ba.

Ana takaddama kan mashigar Hormuz

Mashigar Hormuz, wadda take matsayin muhimmiyar hanyar jigilar kayan mai da makamashi, ta zama babban fagen takaddama tun bayan ɓallewar yaƙin Gabas ta Tsakiya a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Iran ta ba wa tsirarun jiragen ruwa kawai damar ratsawa ta hanyar ruwan, hanyar da a lokacin zaman lafiya ke ɗaukar kashi ɗaya bisa biyar na jigilar mai da iskar gas na duniya, tare da sauran muhimman kayayyaki.

Kara karanta wannan

Yadda ta leko ta koma da Iran ta yi kan mashigar Hormuz ta rikita lissafi a Najeriya

Kafin sanar da samun kuɗaɗen shigar daga harajin, Majalisar dokokin Iran tana ta yanke shawarar ko za ta sanya haraji a kan sufurin jiragen ruwa ta mashigar, yayin da jami’an Iran suka yi gargaɗin cewa zirga-zirgar ababen hawa ta mashigar “ba za ta koma yadda take ba kafin yaƙi”.

Jaridar Vangard ta ce a ranar 30 ga Maris, kafafan yaɗa labaran gwamnatin Iran sun ce kwamitin tsaro na majalisar ya amince da shirye-shiryen sanya harajin, amma ba a fito fili an bayyana ko majalisar ta dauki matakin karshe kan lamarin ba.

Iran ta fara samun kudade daga mashigar Hormuz
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Trump na son a bude mashigar Hormuz

Shugaban Amurka Donald Trump ya kasance yana matsawa Iran lamba domin ta buɗe mashigar ta Hormuz.

Birtaniya, Faransa da masu tsara dabarun soja daga ƙasashe sama da 30 sun gudanar da tattaunawa domin kare zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar, inda Paris da London suka ce za su jagoranci wani aiki na ƙasashe da dama “da zarar yanayi ya ba da dama”.

Amurka ta jawo wa Iran asara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Amurka ta jawo Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta buga asara sakamakon killace tashoshin jiragen ruwanta.

Kakakin fadar White House, Karoline Leavitt ta bayyana cewa Iran na tafka asara sakamakon killace tasoshin jiragen ruwanta da Amurka ta yi.

Karoline Leavitt ta nuna cewa Iran na tafka asarar Dala miliyan 500 a kowace rana sakamakon matakin da Amurka ta dauka na killace tashoshin jiragen ruwanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng