"Mutum 1 Zai Yanke Hukunci," Amurka Ta Bayyana Abin da Take Jira daga Kasar Iran
- Fadar shugaban kasar Amurka, White House, ta musanta rahotannin da ke cewa kwanaki uku zuwa biyar aka kara a wa'adin taagaita wuta
- Ta ce Shugaba Donald Trump ne kadai ke da ikon kayyade lokacin tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran kuma bai yi hakan ba a yanzu
- White House ta kuma jaddada cewa har yanzu Amurka na dakon amsa daga kasar Iran kam sharuddan yarjajeniyar zaman lafiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Fadar White House ta ce Shugaban Amurka Donald Trump bai sanya wani takamaiman wa’adin kawo karshen tsagaita wuta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba.
Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Trump ya sanar da tsawaita tsagaita wutar Amurka da Iran, wacce ya kamata ta kare a yau Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan
Kwana 1 kafin ci gaba da yaki, Shugaban Amurka ya fadi abin da yake tsammani daga Iran

Source: Getty Images
Yaushe wa'adin taagaita wuta zai kare?
Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuna cewa mai magana da yawun fadar, Karoline Leavitt, ta bayyana cewa rahotannin da ke cewa karin wa’adin taagaita wutar bai wuce kwanaki uku zuwa biyar ba, ba gaskiya ba ne.
Ta ce shugaba Trump ne kadai ke da ikon yanke hukunci a karshe kan lokacin da tsagaita wutar zai kare, yayin da yake jiran martani guda daya daga shugabannin Iran kan sharuddan yarjejeniyar zaman lafiya.
Iran ta ki komawa teburin sulhu
Wannan na zuwa ne bayan Iran ta gujewa halartar zaman tattaunawa a zagaye na biyu saboda abin da ta kira keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta yi.
Iran ta bayyana cewa ba za ta koma teburin sulhu ba har sai Amurka ta dakatar da matakin da ta dauka na rufe tashoshin ruwa na kasar Iran.
Mai magana da yawun fadar shugaban Amurka, Leavitt ta ce a halin yanzu ana gwabza rikici tsakanin masu sassaucin ra’ayi da masu tsattsauran ra’ayi a cikin Iran.

Kara karanta wannan
"Babu lokaci," Trump ya sake maganar tashin hankali, ya mika zabin da ya rage ga Iran
Shugaba Trump yana tausayawa Iran
Ta kara da cewa Trump ya nuna sassauci ga Iran ta hanyar amincewa da bukatar tsawaita tsagaita wuta bayan karewar wa'adin makonni biyu, cewar rahoton NBC News.
A cewarta, duk da tsagaita wuta a bangaren soji, Amurka na ci gaba da kakaba matakan matsin tattalin arziki da kuma killace jiragen ruwa na Iran.

Source: Getty Images
Karoline Leavitt ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin tilasta wa kasar Iran ta amince da sharuddan da Amurka ta shimfida son tabbatar da zaman lafiya.
Fadar White House ta jaddada cewa ana jiran cikakken matsaya daga Iran kafin a dauki mataki na gaba kan batun sulhu da kuma makomar rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.
Rasha ta nuna goyon baya ga Iran
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Rasha ta tuna irin tarkon da Amurka ta dana wa kasar Iran yayin tattaunawa kan shirin kera makamin nukiliya a shekarun baya.

Kara karanta wannan
"Abu 1 muke tsoro," Qatar ta tsoma baki kan batun tattaunawar sulhun Amurka da Iran
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov ya ce Iran tana da gaskiya idan ta nuna shakku kan wannan zaman sulhu duba da abin da ya faru a baya.
Ya bayyana cewa Rasha na ci gaba da bibiyar yadda al’amura ke tafiya, yana mai cewa yanayin na iya sauyawa cikin kankanin lokaci.
Asali: Legit.ng