Dan Uwan Netanyahu Ya Mutu a Yaki, Firaministan Israila Ya Yi Jimami
- Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya aika sako na ban tausayi don tunawa da marigayi ɗan uwansa, Yoni Netanyahu
- Yoni Netanyahu, babban jami'in sojan IDF da aka karrama, wanda aka kashe a lokacin aikin ceto na Entebbe a ƙasar Uganda a shekarar 1976
- Firaministan na Israila ya bayyana cewa yana cikin kewar dan uwan na sa tun bayan da aka raba shi da duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Israila - Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya rubuta wani sako mai ratsa zuciya don tunawa da yayansa, Yonatan “Yoni” Netanyahu.
An kashe Yoni Netanyahu ne a lokacin wani babban aikin soja a ƙasar Uganda shekaru da dama da suka gabata.

Source: Getty Images
Benjamin Netanyahu ya tuna da dan uwan nasa ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Talata, 21 ga watan Afirilun 2026.
Benjamin Netanyahu ya tuna da dan uwansa
“Yoni ɗan uwana ne. Jagora na wanda ya taimake ni wajen gano hanya ta a cikin sarkakiya da juyi na rayuwa."
- Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu ya bayyana Yoni a matsayin madubin dubawa da ƙarfin gwiwa, inda ya ƙara da cewa:
“Ba rashin ɗan uwa abin kauna ba ne kawai. Rashin madogara ne. Na kasance da tabbacin cewa ba zan taɓa farfaɗowa ba. Amma da wucewar lokaci, na fahimci cewa abin da Yoni ya yi bai ƙare da mutuwarsa ba.”
An kashe Yoni Netanyahu a aikin Entebbe
Yoni Netanyahu (1946–1976) ya kasance babban jami'in soja da aka karrama sosai a rukunin fitattun sojoji na Isra'ila wato Sayeret Matkal.
An kashe shi ne yayin da yake jagorantar aikin Entebbe (Operation Entebbe), wanda kuma aka sani da Operation Yonatan, wani aikin ceto a ƙasar Uganda wanda ya ’yanta sama da mutane 100 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su.
Netanyahu ya kadu kan mutuwar dan uwansa
A cikin sakon nasa, Netanyahu ya yi tunani a kan yadda dabi'un ɗan uwansa ke ci gaba da zaburar da ƙasashe:
“Matasa sun karanta littafinsa na wasiƙu, mayaka sun samu kwarin gwiwa daga dabi'unsa. Yoni bai bar mana tarihin jarumtaka kawai ba. Ya bar mana hanya."
"Lokacin da na samu labarin cewa Yoni ya mutu a aikin Yonatan don ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, na ji kamar rayuwata ta zo ƙarshe.”
- Benjamin Netanyahu

Source: Twitter
Firaministan na Isra'ila ya kammala saƙonsa da wata magana ta kashin kai ta kewar ɗan uwansa:
“Ina kewarka, Yoni, ɗan uwana abin kauna. Ina kewarka ƙwarai da gaske.”
Israila ta karya yarjejeniya a Lebanon
A wani labarin kuma, kun ji cewa Israila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar kai hare-hare masu muni a Kudancin kasar Lebanon.
Sojojin Isra’ila sun ci gaba da harba manyan bindigu kan garuruwan Khiam da Dibbine da ke kudancin Lebanon bayan fatali da tsagaita wuta.
Munanan hare-haren sun nuna cewa tsagaita wutar da aka sanar ba ta samu cikakken aiwatar wa ba daga ɓangaren Isra'ila ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

