Trump Ya Ci Gaba da Matsa Lamba ga Iran, an Fadi Barnar da Ya Yi Wa Kasar Musulunci

Trump Ya Ci Gaba da Matsa Lamba ga Iran, an Fadi Barnar da Ya Yi Wa Kasar Musulunci

  • Amurka na ci gaba da killace tashoshin jiragen ruwan Jamhuriyar Musulunci ta Iran duk da yarjeniyar tsagaita wutar da aka kulla
  • Kakakin fadar White House ta bayyana cewa tattalin arzikin Iran na fuskantar gagarumar matsala kan matakin da Amurka ta dauka
  • Karoline Leavitt ta bayyana asarar da Iran ke tafkawa a kowace rana sakamakon hana jiragen ruwa shiga ko fita daga tashoshin jiragen ruwa na kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Kakakin fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce Amurka tana yi wa Iran barna mai tsanani a fannin tattalin arziƙi.

Karoline Leavit ta bayyana cewa Amurka na yin hakan yayin da ƙasar Iran ta ƙi amincewa da tattaunawa kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya mai dorewa.

Trump ya jawo asarar miliyoyi ga Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a Oval Office Hoto: Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Karoline Leavit ta bayyana hakan ne yayin tattaunawa da maneman labarai a ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta gindaya sharuɗan sake zama a teburin tattaunawa da Amurka

Wace asara Amurka ta jawo ga Iran?

Karoline Leavit ta bayyana cewa Iran na tafka asara sakamakon killace tasoshin jiragen ruwanta da Amurka ta yi.

“Mun shake tattalin arziƙinsu gaba ɗaya ta hanyar wannan killace su da muka yi, suna asarar Dala miliyan 500 a kowace rana."
"Tsibirin Kharg ya cika maƙil, ba za su iya shigar da mai ko fitar da shi ba. Ba za su iya ko biyan mutanensu ba sakamakon wannan matsin lamba na tattalin arziƙi da Shugaba Trump ya sanya masu."
“Don haka ya gamsu da hakan yayin da muke jiran martaninsu.”

- Karoline Leavitt

Trump na daga kafa ga Iran

Kakakin ta fadar White House ta ce Shugaba Trump ya kasance yana ba da ɗan sassauci cikin karamci ga gwamnatin da aka gurgunta sakamakon aikin soja na Operation Epic Fury” bayan ya sanar da tsawaita tsagaita wuta.

“Wannan fafatawa ce tsakanin masu saukin ra'ayi da masu tsatstauran ra'ayi a Iran a halin yanzu, kuma shugaban yana son samun martani guda ɗaya."

Kara karanta wannan

Iran na ƙara ɗaura ɗamarar yaƙi, ta ce ba za ta lamunci 'zaluncin' Amurka ba

"Don haka yayin da muke jiran wannan martanin, akwai tsagaita wuta ta fuskar soja da hare-hare, amma aikin soja na ‘economic fury’ yana nan yana ci gaba, sannan killace su ta ruwa mai asiri da nasara tana nan tana ci gaba."

- Karoline Leavitt

Yaushe tsagaita wuta za ta zo karshe?

Hakazalika ta ce Shugaba Trump ne zai bayyana lokacin da tsawaita tsagaita wutar da aka yi da Iran za ta ƙare.

Trump zai sanar da lokacin karewar wa'adin tsagaita wuta da Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images
“Shugaban kasa bai kayayyade wani ƙwaƙƙwaran wa'adi ba kamar yadda na gani a wasu rahotanni a yau. Na sani akwai wasu rahotannin majiyoyin da ba a bayyana sunansu ba suna cewa akwai tazarar kwanaki uku zuwa biyar. Wannan ba gaskiya ba ne."

- Karoline Leavitt

Ta ƙara da cewa, shugaban na Amurka yana jiran “martani guda ɗaya” ne daga shugabannin Iran game da sharuɗɗan Amurka na yarjejeniyar zaman lafiya.

Iran ta gindaya sharuddan zama da Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gindaya sharuddan sake zama teburin sulhu don tattaunawa da Amurka.

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya ce za su tattauna ne idan Amurka ta kawo karshen aikin killace tashoshin jiragen ruwan kasar.

Iravani ya bayyana cewa matakin na Amurka ya karya yarjejeniyar tsagaita wuta da ake ta kokarin samarwa a tsakanini kasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng