Babbar Magana: Trump Ya Sake Sabon Ikirari kan Mashigar Hormuz

Babbar Magana: Trump Ya Sake Sabon Ikirari kan Mashigar Hormuz

  • Ana ci gaba da takaddama tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan mashigar ruwa ta Hormuz
  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa sojojin ruwan kasarsa sun karbe iko da mashigar Hormuz wadda Iran ta kulle
  • Donald Trump ya kuma bayyana tsawon lokacin da mashigar ta Hormuz za ta yi a karkashin ikon dakarun sojojin ruwan Amurka

​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan mashigar Hormuz da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta rufe.

Shugaba Trump ya ce Amurka tana da cikakken iko a kan mashigar ruwa ta Hormuz, wadda take matsayin muhimmiyar hanyar jigilar ɗanyen mai a teku.

Trump ya yi ikirari kan mashigar Hormuz
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a Oval Office Hoto: Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Iran ta fara cin gajiyar kulle mashigar Hormuz duk da matsin lambar Amurka

Ana takaddama tsakanin Amurka da Iran

An kwashe lokaci ana takaddama kan ikon hanyar ruwan tun lokacin da yaƙi ya ɓalle tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila a watan Fabrairun 2026.

Kulle mashigar da Iran ta yi ya nakasa jigilar mai a duniya baki ɗaya, lamarin da ya yi sanadiyar tashin farashi tare da tilasta wa gwamnatoci ɗaukar tsauraran matakan rage amfani da makamashi.

Jaridar TheCable ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen da ke yaƙi da juna ta kai ga Iran ta ayyana buɗe mashigar Hormuz ga zirga-zirgar jiragen kasuwanci. Sai dai an soke hakan ƙasa da sa'o'i 24 bayan yin ta.

Kasar Iran ta yi zargi kan Amurka

Iran ta zargi Amurka da "fashi a teku" biyo bayan shawarar da Trump ya yanke na ci gaba da killace mashigar da dakarun sojojin ruwan Amurka suka sanar a wannan makon, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Har yanzu Iran ba ta sanar da sake buɗe mashigar ba, yayin da dakarun sojin ruwan Amurka suke ci gaba da kasancewa a kewayen hanyar ruwan.

Kara karanta wannan

Trump ya ci gaba da matsa lamba ga Iran, an fadi barnar da ya yi wa kasar Musulunci

Me Trump ya ce kan mashigar Hormuz?

A wani saƙon da ya wallafa, Trump ya yi iƙirarin cewa Amurka ce ke da iko a kan mashigar ruwan, yana mai cewa Iran tana fuskantar "lokaci mai wahala" wajen gano ko wanene shugabansu.

“Muna da cikakken iko a kan mashigar Hormuz. Babu wani jirgin ruwa da zai iya shiga ko fita ba tare da amincewar rundunar sojojin ruwa ta Amurka ba."

- Donald Trump

Trump ya ƙara da cewa za a tsaurara rufe mashigar har zuwa lokacin da Iran za ta iya cimma yarjejeniya.

Ana takaddama tsakanin Amurka da Iran kan mashigar Hormuz
Wani babban jirgin ruwa na shirin wucewa ta mashigar Hormuz Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

A wani saƙo na daban, Trump ya bayyana cewa ya ba rundunar sojojin ruwa ta Amurka umarnin harbin duk wani jirgin ruwa da ke dasa "nakiya" a cikin ruwan mashigar Hormuz.

A halin da ake ciki, Iran ba ta kai ga mayar da martani kan kalaman Trump na cewa Amurka ce ke da ikon sarrafa mashigar Hormuz ba.

Iran ta fara samun kudin shiga

Kara karanta wannan

Iran ta sabunta makamai yayin tsagaita wuta da Amurka, tana shirin ko ta kwana

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara samun kudaden shiga sakamakon kulle mashigar ruwa ta Hormuz.

Wani babban jami’in majalisar dokokin Iran, Hamidreza Hajibabaei, ya bayyana cewa Tehran ta karɓi kuɗaɗen shiga a mashigar ruwa ta Hormuz.

Jami'in wanda yake da matsayin Mataimakin shugaban majalisa ya bayyana cewa an karbi kudaden shiga na farko daga harajin da Iran ta sanyawa mashigar ruwa ta Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng