NiMet Ta Jero Gombe, Kano da Wasu Jihohin Arewa da za a Tsula Ruwan Sama
- Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama a sassa daban-daban na Najeriya a yau, Litinin, 17 ga Agusta, 2026
- Ana sa ran ruwan sama zai ƙara yawaita daga rana zuwa yamma, musamman a jihohin Arewa ta Yamma, Arewa ta Tsakiya da Kudancin ƙasar
- NiMet ta bayyana hakan ne a cikin hasashen yanayin da ta fitar kan yanayin da ake sa ran samu daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa 11:59 na daren yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - NiMet ta yi hasashen cewa wasu sassan jihohin Gombe, Borno, Bauchi, Adamawa da Taraba za su fuskanci gajimare da tsawa tare da ruwan sama a safiyar yau.
Da rana zuwa yamma, ana sa ran tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Borno, Gombe, Bauchi, Yobe, Adamawa da Taraba.

Source: Facebook
A sakon da ta wallafa a Facebook, hukumar ta ce hakan na nufin ruwan sama zai ƙaru daga baya da rana, inda tsawa za ta shafi wasu sassan jihohin Arewa.
Hasashen a Arewa ta Tsakiya
A jihohin Arewa ta Tsakiya, NiMet ta yi hasashen samun gajimare da tsawa tare da ruwan sama mai sauƙi a safiya a wasu sassan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nasarawa, Benue da Plateau.
Daga rana ta yi zuwa yamma, ana sa ran matsakaicin ruwan sama a mafi yawan sassan jihohin Arewa ta Tsakiya.
Hakan na nufin wasu wurare za su fara yini cikin yanayi mai gajimare da danshi, yayin da ruwan sama zai ƙara yaɗuwa daga rana zuwa yamma.
Za a yi ruwa a jihohin Kudu
A Kudancin Najeriya, ana sa ran gajimare da ruwan sama mai sauƙi da safiya a wasu sassan Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

Kara karanta wannan
Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu
Da rana zuwa yamma, NiMet ta yi hasashen samun matsakaicin ruwan sama a faɗin jihohin Kudancin Najeriya. Hukumar ta ce yanayin damina zai ƙara yaɗuwa a sassan yankin daga baya da rana.

Source: Getty Images
Gargadin NiMet ga jama'a
NiMet ta yi gargadin cewa iska mai ƙarfi na iya gabatar da tsawa, sannan ta buƙaci mazauna wuraren da ambaliyar ruwa ke yawan faruwa, wuraren da suke ƙasa da kuma wuraren da ba su da ingantaccen magudanar ruwa da su kasance cikin shiri.
Haka kuma, hukumar ta shawarci masu abubuwan hawa da su yi taka-tsantsan yayin ruwan sama tare da guje wa hanyoyin da ambaliyar ruwa ta mamaye.
An kuma shawarci jama'a da su cire kayan lantarki daga wuta yayin tsawa idan ya zama dole, yayin da masu zirga-zirgar jiragen sama suka kamata su nemi rahotannin yanayi na musamman na filayen jiragen sama.
An yi wurin rarraba abinci a Legas
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Jihar Legas ta ƙaddamar da sabon cibiyar kasuwancin abinci a Agege domin rage asarar amfanin gona bayan girbi da inganta tsarin rarraba abinci.
Cibiyar, wadda ke Pen Cinema, an tsara ta ne domin karɓar ’yan kasuwa tsakanin 350 zuwa 400 tare da samar da wuraren ajiya da kasuwanci ga manoma, masu tattara amfanin gona, ’yan kasuwa da sauransu.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce aikin wani ɓangare ne na dabarun magance matsalolin tsarin samar da abinci a Legas, maimakon dogaro kawai da ƙara yawan samar da abinci.
Asali: Legit.ng
