Babbar Magana: Trump Ya Yi Barazanar Kai Wa Kawar Amurka Mummunan Hari
- Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Oman mummunan hari idan ta kawo cikas ga yarjejeniyar Amurka da Iran kan mashigar Hormuz
- Trump ya bukaci Iran ta mika wuya, yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da tattaunawa kan makomar mashigar
- Iran ta ce mashigar Hormuz, wadda take da muhimmanci ga jigilar makamashi a duniya, za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikonta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa kasar Oman hari wadda take kawa ce ga Amurka.
Trump ya yi wa Oman barazanar kai hari ne idan ta kawo cikas ga kokarin Washington na cimma yarjejeniya da Iran kan sarrafa zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Source: Getty Images
Trump ya yi barazana ga Oman
Trump ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da ɗan jaridar Fox News, Trey Yingst, wadda ya sanya a shafinsa na X.
A yayin hirar, Trump ya yi magana kan tattaunawar da Oman da Iran ke yi game da makomar zirga-zirgar ruwa a mashigar.
“Idan Oman ta kawo cikas, za mu kai musu mummunan hari,” Trump ya ce, yana magana kan tattaunawar da ke gudana tsakanin Oman da Iran, yayin da Washington ita ma ke kokarin yin nata tattaunawar da Tehran.
Jami’an Iran da Oman sun shafe makonni suna tattaunawa kan tsarin zirga-zirgar jiragen ruwa a nan gaba ta mashigar, yayin da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana a ranar Litinin cewa kasashen biyu na aiki kan wata sanarwar hadin gwiwa.
Sai dai Trump ya sha nanata cewa mashigar Hormuz tana ƙarƙashin ikon Amurka, duk da cewa zirga-zirgar jiragen ruwa ta ragu sosai tun bayan da Iran ta kusan rufe mashigar a farkon yakin Gabas ta Tsakiya a ranar 28 ga Fabrairu.
Iran ta ce tana da iko da mashigar Hormuz

Kara karanta wannan
Amurka ta daina boye boye, ta bayyana manufofi 2 da take son cimmawa a yaki da Iran
A ranar Juma’a, Trump ya yi ikirarin cewa har zai iya ayyana mashigar Hormuz a matsayin wani yanki na ƙasar Amurka.
Iran ta mayar da martani da cewa mashigar ruwan da take da matuƙar muhimmanci kuma ta toshe zirga-zirga a cikinta “za ta ci gaba da kasancewa ta Iran”.
Kafin fara yakin Amurka da Isra’ila da Iran, ana ɗaukar mashigar Hormuz a matsayin hanyar ruwa ta kasa da kasa da kowa ke da damar amfani da ita.
Trump ya bukaci Iran ta mika wuya
Trump ya kuma ce ya kamata Iran ta “daga farar tuta ta mika wuya”, kamar yadda Yingst ya wallafa a shafinsa na X yayin da yake bayyana abin da shugaban ya fada a hirar.
Duk da rashin farin jinin yakin a tsakanin Amurkawa, musamman gabanin zaben tsakiyar wa’adin mulkin Amurka na Nuwamba, Trump ya ce ba ya cikin gaggawar cimma yarjejeniya da Iran.
Jam’iyyar Democrats mai adawa da Trump na kokarin kwace ikon Majalisa daga hannun jam’iyyar Republicans ta Trump a zaben.
Trump ya kuma shaida wa Yingst cewa akwai wata kafar sadarwa ta sirri kai tsaye tsakanin gwamnatinsa da jami’an Rundunar Kare Juyin Juya Hali ta Iran.

Kara karanta wannan
Da gaske ne: Trump ya tabbatar da fargabar harin Iran, ya yi basaja a cikin jirgi
An ruwaito Trump yana cewa:
“Su ƙwararrun ‘yan wasan caca ne, amma suna mutuwa.”

Source: Getty Images
Abubuwan da Amurka ke son samu a yaki da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasarr Amurka, JD Vance, ya bayyana cewa manufofin Amurka a yakin da take yi da Iran sun kasu gida biyu.
JD Vance ya bayyana manufofin guda biyu da Amurka ke son cimmawa a yaki da Iran shafi tattalin arziki da soji.
Asali: Legit.ng
