Trump Ya Yi Azarbabi, Ya Fadi Kalar Yarjejeniyar da Za a Kulla da Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan kalar yarjejeniyar da za a kulla da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Donald Trump ya bayyana cewa za a kulla yarjejeniyar da za a kulla za ta fi ta baya wadda aka kulla a shekarar 2026
- Shugaba Trump ya kuma soki magabatansa Barack Obama da Joe Biden kan yadda suka tafiyar da yarjejeniya da kasar Iran
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan yarjejeniyar da za a kulla da Iran.
Shugaba Trump ya bayyana cewa Amurka za ta kulla yarjejeniya mai kyau da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Litinin, 20 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Trump ya saki baki, ya bayyana abin da zai iya faruwa a zama na 2 tsakanin Amurka da Iran
Me Trump ya ce kan yarjejeniya da Iran?
Shugaba Donald Trump ya yi iƙirarin cewa yarjejeniyar da Amurka ke “ƙullawa da Iran za ta fi JCPOA kyau nesa ba kusa ba."
JCPOA dai wata gagarumar yarjejeniyar nukiliya ce da gwamnatin Iran da manyan ƙasashen duniya suka rattabawa hannu, ciki har da Amurka, a shekarar 2015.
A shekarar 2018, lokacin wa’adinsa na farko, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliya ta 2015 tare da kakaba takunkumai masu tsanani, waɗanda suka raunana tattalin arziƙin Iran.
Trump ya soki Obama da Biden
A cikin saƙon da ya wallafa, Trump ya soki magabatansa Barack Obama da Joe Biden, sannan ya ci gaba da cewa yarjejeniya a ƙarƙashinsa za ta tabbatar da “zaman lafiya da tsaro, ba wai kawai ga Isra'ila da Gabas ta Tsakiya ba, har ma ga Turai, Amurka, da ko'ina”.
"Yarjejeniyar da muke yi da Iran za ta fI JCPOA kyau ne sa ba kusa ba, wadda aka fi sani da “Yarjejeniyar Nukiliyar Iran,” wadda Barack Hussein Obama da Sleepy Joe Biden suka rubuta, ɗaya daga cikin mafi munanan yarjejeniyoyin da aka taɓa yi game da tsaron kasarmu."
"Hanya ce tabbatacciya ta samun makamin nukiliya, wanda ba zai faru ba, kuma ba zai taɓa yiwuwa ba tare da yarjejeniyar da muke aiki a kai."
"Sun ma ba da Dalar Amurka Biliyan 1.7 a tsabar kuɗi, aka loda a cikin jirgin Boeing 757, aka kai Iran don shugabannin Iran su kashe duk yadda suka ga dama."
"Ya kwashe dukkan tsabar kuɗin daga bankuna a D.C., Virginia, da Maryland. Waɗancan ma'aikatan banki sun ce ba su taɓa ganin irin wannan ba a baya."
"Bugu da ƙari, an biya Iran daruruwan biliyoyi na daloli. Idan ban soke wannan “yarjejeniya” ba, da an yi amfani da makaman nukiliya a kan Isra'ila, da ko'ina a Gabas ta Tsakiya, ciki har da sansanonin sojojin Amurka da muke ƙauna."
- Donald Trump

Source: Facebook
Trump ya fadi dalilin yaki da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana dalilin yaki da Iran.
Shugaba Trump ya bayyana cewa ba kasar Israila ba ce ta sanya ya fara yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaban na Amurka ya bayyana cewa burinsa na rashin son ganin Iran ta mallaki makamin nukiliya ya sanya ya fara yaki da kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
