Duk da Kalaman Trump, Iran Ta Fito da Gaskiyar Abin Ya Kawo Cikas a Tattaunawa da Amurka
- Iran ta bayyana cewa halayen da Amurka ta nuna na karya alkawari ne suka kawo tangarda a zaman tattaunawar da ake yi a Pakistan
- Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya tattauna da takwaransa na Pakistan, Ishaq Dar ta wayar tarho yau Litinin
- Araghchi ya shaida masa cewa karya yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta yi ne ya sa Iran ja da baya daga bukatar komawa tattaunawa ta biyu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Gwamnatin kasar Musulunci ta Iran ta ce karya ka'iodji da sharuddan yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta yi, shi ne asalin abin da ya kawo tsaiko a tattaunawar sulhu.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta waya da takwaransa na Pakistan, Ishaq Dar yau Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan
"Ta yaudare mu sau 2," Iran ta sake tona asirin Amurka ana shirin komawa teburin sulhu

Source: Getty Images
Ya ce Iran za ta yanke hukunci kan matakin da za ta ɗauka a gaba, bayan nazarin dukkanin abubuwan da ke faruwa, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Pakistan ke ci gaba da kokarin shawo kan kowane bangare domin komawa zagaye na biyu na tattaunawa a birnin Islamabad.
Amurka dai ta amince da komawa teburin sulhun har ta tura wakilanta amma Iran ta nuna shakku kan lamarin saboda abin da ta kira yaudarar da aka yi mata a baya.
Sharaɗin Iran kan tattaunawa
Iran ta jaddada cewa ba za ta shiga sabuwar tattaunawa ba har sai an ɗage takunkumin da Amurka ta kakaba mata a tashoshin ruwa.
Sai dai masu shiga tsakani daga Pakistan sun isar da saƙo cewa Amurka ba ta da niyyar janye wannan mataki a yanzu, lamarin da ya sa Iran ta kaucewa shirin sake zama a yau Litinin.

Kara karanta wannan
Iran ta jingine batun zaman sulhu bayan Amurka ta kai wa jirginta hari, ta shirya ramuwa
Duk da haka, akwai yiwuwar bangarorin biyu su sassauta matsayar tasu kamar yadda aka gani a baya kan batun Lebanon.
Haka zalika, ana hasashen cewa Iran na iya amincewa da tattaunawa idan Amurka ta sassauta takunkumai da ta kakaba mata
Sai dai shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ba za a matsa wa ƙasarsa lamba ba domin shiga tattaunawa, kamar yadda NBC News ta kawo.
Iran ta dora laifi a kan Amurka
Da yake hira da takwaransa na Pakistan kan halin da ake ciki, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya zargi Amurka da halaye marasa kyau da kuma saɓani a kalaman shugabanninta.

Source: Getty Images
Ya ce kalaman Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na cin karo fa juna, lamarin da yake ganin ba su dace da da’awar neman diflomasiyya ba.
Iran ta ce za ta ci gaba da lura da matakan da ɓangaren Amurka ke ɗauka kafin ta yanke hukuncin da ya dace domin kare muradunta da tsaron ƙasa.
Ana sa ran sulhun Iran da Amurka

Kara karanta wannan
Bayan ta kekashe kasa, Amurka ta gabatar da sabon tayi ga kasar Musulunci ta Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa kasar Amurka da Iran za su cimma matsaya kuma su rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu yau Litinin.
Shugaba Trump ya kuma tabbatar da cewa tawagar Amurka karkashin jagorancin mataimakinsa, JD Vance na kan hanyarta zuwa Islamabad.
Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa yana shirye ya gana da manyan shugabannin Iran idan aka samu ci gaba a tattaunawar da ake yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng