Labaran garkuwa da mutane
Wasu yan bindiga da ake zargin yan Fulani makiyaya ne, sun kai hari wani ƙauye dake yankin ƙaramar hukumar Agatu jihar Benuwai, sun samu nasarar kashe mutum 27.
Wasu yan bindiga sun hallaka mutane aƙalla 26 a wani mummunan hari da suka kai ƙauyukan jihar Zamafa, an fafata tsakanin su da jami'an yan sanda dake yankin.
Wasu yan bindiga sun kutsa kai har cikin gidan Hakimin Zungeru, Alhaji Mustapha Madaki, inda suka yi awon gaba da shi, tare da matan sa biyu, a jihar Neja.
Iyayen Ɗaliban da aka sace a jihar Neja sun shiga cikin wani sabon tashin hankali yayin da aka tsinci gawar ɗaya daga cikin ƴaƴansu da yan bindiga suka sace.
Wasu yan bindiga haye akan mashina 60 sun kai hari ƙauyukan Kanawa da Runka, ƙaramar Hukumar Ɗanmusa jihar Katsina, inda suka kashe mutum 6 tare da jikkata wasu
Jami'an hukumar yan sanda a yankin Ugba na jihar Benuwai, sun samu nasarar hallaka yan fashi da makami biyar da suka addabi garin watanni da dama da suka wuce.
Wasu yan bindiga sun hallaka mutum uku tare da jikkata wasu da dama akan Hanyar zariya zuwa Kaduna. Hakanan wasu yan bindiga sun kashe mutum biyu a Ƙauyen Kabai
Yan bindigan da Suka yi awon gaba da wata motar bas ta makaranta a Ondo, sun saki ma'aikaciyar dake cikin motar mai suna Omolayo Ojo ranar alhamis da safe.
Wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da motar bas din makaranta a jihar Ondo. Babu dalibai cikin bas din, amma sun sace motar da wata jami'ar makarantar dake ciki
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari