Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah

- Wasu yan Bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun yi awon gaba da shugaban ƙungiyar fulani ta Miyetti Allah reshen jihar Kogi

- Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sunje har gidansa, sannan suka tilasta masa tafiya tare da su

- Sakataren ƙungiyar ya bayyana cewa tunda aka sanar dashi abinda ya faru yake neman lambar wayar shugaban nasu amma baya samunsa, daga baya akace wayar na kashe

Wasu yan bindiga sun sace shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah, MACBAN, reshen jihar Kogi, Wakili Damina, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ku Ƙara mana Lokaci kar ku kashe 'yayan mu, Iyayen Ɗalibai sun Roƙi yan Bindiga

Sakataren MACBAN na jihar Kogi, Adamu Abubakar, shine ya faɗawa manema labarai hakan ranar Talata a Lokoja.

Yace shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigar sun zo a wata farar motar Bas, da misalin ƙarfe 12:00 na yamma suka yi awon gaba da shugaban daga gidansa.

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Fulani Miyetti Allah
Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Fulani Miyetti Allah Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Abubakar yace ƙanin Ɗamina ya faɗa masa abunda ya faru awa ɗaya bayan faruwarsa, wanda a cewarsa a gabansa akai komai.

Sakataren ya ƙara da cewa yayi gaggawar kiran lambar wayan shugaban amma ba'a ɗauka ba har ta gama ringin. Yace da ya sake kiran lambar bayan awa ɗaya sai yajita a kashe.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani

Sakataren yace:

"Tun bayan da na samu labarin sace shugaban, nake ta kiran layin wayarsa amma bata shiga, kuma duk wani ƙoƙari na gano inda yake yaci tura."

"Daga nan, nayi gaggawar sanar da kwamishinan yan sandan jihar kan abinda ke faruwa, haka kuma itama gwamnatin jihar an sanar da ita ta ofishin mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Mr Jerry Omodara."

Da aka tuntuɓi kwamishinan yan sandan jihar, Ede Ayuba, yace har yanzun rundunar yan sanda bata gano ainihin inda shugaban MACBAN din yake ba.

A wani labarin kuma Gwamnatin Kogi Tayi Cikakken Bayani Kan Kisan da Yan Bindiga Suka Yiwa Kwamishinanta

Gwamnatin jihar Kogi tayi jawabi a kan harin da aka kaima kwamishinan ta da kuma wani shugaban ƙaramar hukuma.

Gwamnatin ta tabbatar da kai harin, inda ta bayyana cewa kwamishinan hukumar fansho ya rasa ransa a harin, kuma an yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel