Madalla! Daliban Jami’ar FUAM da Aka Sace a Jihar Benuwai Sun Kuɓuta

Madalla! Daliban Jami’ar FUAM da Aka Sace a Jihar Benuwai Sun Kuɓuta

- Ɗaliban jami'ar koyon aikin gona FUAM ta jihar Benuwai waɗanda aka sace kwanakin baya sun kuɓuta

- Hukumar makarantar FUAM ta tabbatar da dawowar ɗaliban ta bakin daraktan yaɗa labaranta, tace ɗaliban na amsar kulawa ta musamman yanzun haka

- Kakakin rundunar yan sandan jihar Benuwai, DSP Catherine Anene, ya tabbatar da kuɓutar ɗaliban, kuma yace ba'a biya kuɗin fansa ba

Ɗaliban da aka sace daga jami'ar koyon ilimin aikin gona (FUAM) jihar Benuwai sun kuɓuta, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta

Daraktan yaɗa labarai da al'amuran yau da kullum na jami'ar, Mrs Rosemary Waku, ita ce ta bayyana hakan a ranar Laraba.

Ta ce ɗaliban da wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba suka yi awon gaba dasu sun samu kuɓuta.

Madalla! Daliban Jami’ar FUAM da Aka Sace a Jihar Benuwai Sun Kuɓuta
Madalla! Daliban Jami’ar FUAM da Aka Sace a Jihar Benuwai Sun Kuɓuta Hoto: channelstv.com
Asali: Twitter

Waku tace biyu daga cikin ɗaliban da aka sace ɗin sun kuɓuta ne ranar Talatan da ta gabata, yayin da sauran suka dawo daga hannun 'yan bindigar da sanyin safiyar Laraba.

A bayanin da daraktan yaɗa labaran tayi bayan dawowar ɗaliban tace:

"Ɗaliban jami'ar FUAM da aka sace kwanakin baya sun kuɓuta. Amma an sako biyu daga cikinsu; Israel Farren Kwaghgee da Solomon Salifu tun jiya 27 ga watan Afrilu."

"A yanzun haka ɗaliban suna amsar kulawa ta musamman bayan dawowarsu daga hannun waɗanda suka sace su."

KARANTA ANAN: Gwamnan Rivers Ya Caccaki APC, Yace Babu Wani Mai Hankali da Zai So APC a 2023

Har ila yau, kakakin 'yan sandan jihar Benuwai, DSP Catherine Anene, ya tabbatar da dawowar ɗaliban a wani ɗan gajeren saƙo da ya fitar.

Yace: "Ɗaliban da aka sace daga makarantar koyon ilimin aikin gona (FUAM) sun kuɓuta ba tare da an jikkata su ba. Kuma jami'an yan sanda na cigaba da bincike a kan lamarin."

Anene ya ƙara da cewa ba'a biya ko naira ɗaya da sunan kuɗin fansa ba kafin a sake su.

Dukkan hukumomin sun yi gum da bakinsu kan matakan da aka bi wajen kuɓutar da ɗaliban, waɗanda da farko 'yan bindigan suka nemi a biya 21 miliyan kuɗin fansa.

A wani labarin kuma Lokaci yayi da zamu nemi taimako, Saraki ya baiwa shugaba Buhari shawara

Tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya shawarci shugaba Buhari da ya nemi taimako daga duk inda yake tsammanin za'a taimaka masa.

Yace Najeriya na cikin wani yanayi da dole sai gwamnati ta nemi taimako domin abun yafi ƙarfinta, kuma hakan ba yana nuna gazawarta bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel