Yadda aka Nemi Ceto Malamar Islamiyya amma Mutane Suka Taru Suka Kashe Ta
- Ana cigaba da samun bayanai game da malamar Islamiyyar da wasu mutane suka yi wa kisan gilla ba tare da aikata laifi ba a jihar Kaduna
- Mijin malamar da wasu daga cikin 'yan uwanta sun yi bayani game da wasu abubuwan da suka faru a lokacin da aka yi yunkurin kashe ta
- Rundunar 'yan sanda ta bayyana matakan da ta dauka a karon farko bayan tabbatar da kisan Malama Ummulkhairi a unguwar Maraban Jos
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Iyalan Malama Ummulkhair, malamar makarantar Islamiyya da wasu mutane suka yi wa kisan gilla tare da ƙona gawarta sun yi magana da manema labarai.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a Maraban Jos da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna bayan zarginta da satar yara.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa wasu mazauna yankin sun zargi Ummulkhair, mai yara huɗu, da yunƙurin satar 'ya'ya yayin da take kan hanyarta ta zuwa wajen karatun addini a ranar Lahadi da rana.
Yadda aka kai mata hari
Hakimin Sabon Maraban Jos, Suleiman Isa, wanda ya shiga cikin ƙoƙarin ceto matar, ya ce mijin Ummulkhair ne ya kira shi yana neman taimako.
"Wani abokina wanda shi ne mijin matar ya kira ni ya sanar da ni abin da ke faruwa. Mutane sun zarge ta da satar yara yayin da take kan hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya domin sauraron wa'azi,"
In ji shi.
Isa ya bayyana cewa ya garzaya wurin da baburinsa domin ceton ta tare da kiran 'yan sanda.
"Na samu damar shiga wurin da aka tsare ta. Daga nan muka kira 'yan sanda saboda jama'a da yawa sun taru. Da isowar 'yan sanda muka samu damar kai ta ofishin 'yan sanda,"

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano
In ji shi.
Hakimin ya ce Ummulkhair ta roƙe shi ya samo mata ruwa, amma bai samu damar yin hakan ba saboda hargitsin da ya biyo baya. Ya ce duk roƙon da shi da malaminta na Islamiyya suka yi wa jama'ar su bari doka ta yi aikinta bai yi tasiri ba.
"Daga baya na sake shiga ofishin 'yan sanda ta ƙofar baya inda take zaune, amma ban same ta ba. Da na fito waje sai na tarar an riga an kashe ta,"
In ji shi.
Maganar mijin malamar Islamiyya
A wani bidiyo da shafin labari da Gaskiya ya wallafa a Facebook, Aliyu Mohammed, ya ce mutuwar matarsa ta jefa shi cikin ruɗani da baƙin ciki.
"Ina cikin ruɗani da takaici saboda ba ta yi wani laifi ba. Malamar Islamiyya ce kuma tana kan hanyarta ta zuwa wani darasin addini ne lokacin da mutane suka tare ta suka zarge ta da satar yara,"

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An rushe katafaren gidan kasurgumin mai garkuwa da mutane da aka cafke a Edo
Inji shi.
Mijin ya ce yanzu ya rage shi kaɗai da kula da yaransu.
"Abin da ya fi bani ciwo yanzu shi ne na rage ni kaɗai da yara. Duk lokacin da na kalle su sai na yi kuka. A daren jiya, ƙaramin yaronmu mai shekara huɗu yana ta tambayar dalilin da ya sa mahaifiyarsa ba ta dawo gida ba, ni kuma sai na yi ƙoƙarin kwantar masa da hankali,"
In ji shi.

Source: Original
'Yar uwar malamar ta yi magana
'Yar'uwar mijin marigayiyar, Zainab Aliyu, wadda ta ce tana tare da Ummulkhair a cikin ofishin 'yan sanda, jami'in kula da ofishin 'yan sanda na yankin ya fito da marigayiyar duk da gargadin da ta yi masa.
"Lokacin da lamarin ya faru muna cikin ofishin 'yan sanda. Mutane suna jifar 'yan sanda da duwatsu, su kuma 'yan sanda suna harba barkonon tsohuwa,"
"Wani Jami'i ya shigo ya tambayi inda wadda ake zargi take. Na nuna masa ita. Sai ya kama hannunta ya fara tafiya da ita. Da muka kusa isa ƙofar fita, na gargadi jami'in cewa jama'a za su kashe ta idan ya kai ta waje."
'Yan sanda sun kama mutane
A wani labarin, mun kawo muku cewa, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kama wasu da ake zargi da hannu a kashe malamar Islamiyya.
Jami'an 'yan sandan sun bayyana cewa ana cigaba da bincike domin kama sauran wadanda ake zargin kuma za a masu hukuncin da ya dace da su.
Biyo bayan lamarin, kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna ya bukaci jama'a da su guji daukar doka a hannu tare da mika rahoto ga hukumomi.
Asali: Legit.ng
