Ku Kare Kanku Daga Harin ’Yan Bindiga, Gwamna Matawalle Ga ’Yan Zamfara

Ku Kare Kanku Daga Harin ’Yan Bindiga, Gwamna Matawalle Ga ’Yan Zamfara

- Gwamnatin jihar Zamfara ta bai wa 'yan jihar damar kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga

- Gwamnatin jihar Zamfara kuma ta tabbatar da kame wasu 'yan ta'adda 35 a wasu yankunan jihar

- Hakazalika ta dage dokar da ta sanya na haramta hada-hadar kasuwanci a wasu yankunan jihar

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi kira ga mazauna yankin da su kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga amma su tabbatar ba su karya doka ba, Channels Tv ta ruwaito.

Yankin Arewa-maso-Yamma na daya daga cikin yankunan da 'yan ta'adda suka fi addabar al'umma.

"Mutane kada su dauki doka a hannunsu ba, amma ya kamata su dauki matakan doka yadda ya kamata don kare al'ummominsu yayin da wasu gungun 'yan ta'adda suka afka musu," in jiwata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Ibrahim Magaji Dosara ya fitar a ranar Laraba.

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana

Ku kare kanku daga harin 'yan bindiga, gwamna matawalle ga 'yan Zamfara
Ku kare kanku daga harin 'yan bindiga, gwamna matawalle ga 'yan Zamfara Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

"Gwamnatin jihar ta amince da mutanen da ke kusa da yankunan 'yan ta'addan da ke cikin jihar da su fito kwansu da kwarkwatansu domin kare kansu a duk lokacin da 'yan ta'addan suka far wa al'ummarsu."

Sanarwar ta kuma sanar da cewa ‘yan sanda sun cafke masu aikata laifuka 35 “wadanda suka hada da galibin masu satar mutane, masu ba da bayanai da wadanda ke taimaka wa ‘yan bindiga a jihar.”

“An yi masu tambayoyi kuma sun amsa laifuffukansu daban-daban kuma tuni aka tura su Abuja don ci gaba da bincike kafin a hukunta su.”

Hakanan, gwamnatin jihar ta ce ta dage haramcin da aka sanya kan harkokin kasuwanci a kasuwanni hudu a jihar.

“Matakin ya biyo bayan kiraye-kiraye da dama daga wasu 'yan kasa da ke damuwa a ciki da wajen jihar, don dage haramcin tare da bai wa talaka damar samun bukatunsa na yau da kullun a cikin watan Ramadana.

"Kasuwannin da abin ya shafa su ne Magami, Wanke, Dansadau da Dauran,” in ji sanarwar.

"An hana kasuwannin hudu yin kowane irin hada-hada a makon da ya gabata bayan hare-hare da kisan mutane da basu ji ba basu gani ba a cikin al'ummomin da abin ya shafa."

KU KARANTA: Buhari Bai da Damu da Halin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki Ba, PDP Ta Caccaki Buhari

A bangare guda, Wani dan majalisar tarayya a ranar Alhamis ya ce Majalisar Dokoki ta kasa za ta bijiro da batun tsige Shugaba Muhammadu Buhari idan bangaren zartarwa ba ta yi aiki da kudurin ta na tsaro ba.

Majalisar wakilai a ranar Laraba ta kaddamar da wani kwamiti na mutune 40 don samar da mafita ga kalubalen tsaron kasar. Kwamitin zai shirya taron kwanaki hudu na tsaro a watan Mayu.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily, dan majalisar mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas a majalisar Tarayya, Dachung Bagos ya ce za a bijiro da batun tsigewar ne idan ba a zartar da kudurorin taron koli ta bangaren zartarwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel