'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani DPO da Jami’ansa 8 a Wata Jihar Arewacin Najeriya
- An ruwaito cewa, 'yan bindiga sun hallaka wani DPO na rundunar 'yan sanda tare da jami'ansa takwas
- DPO ya samu labarin hari ne, inda ya gaggauta kai dauki wanda anan ya gamu da ajalinsa da jami'ansa
- An nemi taimakon sojin saman Najeriya, yayin da suka gaggauta kawo dauki zuwa yankin a jihar Kebbi
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani DPO da jami'ansa takwas a Jihar Kebbi da ke arewacin kasar.
Kakakin 'yan sandan na Jihar Kebbi ASP Nafi'u Abubakar ne ya tabbatarwa BBC faruwar lamarin, wanda ya faru a ranar Lahadin da ta gabata.
"Da misalin karfe 2:30 na rana ne DPO na Kasaba ya samu labarin an kai hari wani kauye da ake kira Makuku da wasu kauyuka da ke kewaye da shi, nan da nan ya debi yaransa su takwas da nufin kai dauki bayan fafatawa kuma anan suka gamu da ajalinsu," in ji ASP Nafi'u.
KU KARANTA: El-Rufa'i Ya Yi Allah Wadai da Harin 'Yan Bindiga a Coci, Ya Mai da Martani
Rahotanni sun ce Sanata mai wakiltar yankin Bala ibn Na'alla ya nemi taimakon rundunar sojin sama, inda nan da nan jirgin yaki ya kawo dauki tare da fatattakar 'yan bindigar, sai dai babu rahoton kashe kowa cikinsu.
Ko a ranar Talatar da ta gabata Sai da 'yan bindiga suka afkawa kauyukan Kunduru da Bajida da Rafin Gora inda suka yi awon gaba da shanu da dama.
A yanzu haka mutanen kauyukan sun fara tserewa daga muhallansu domin tsira da rayukansu.
KU KARANTA: Allah-wadai: Biyo bayan kashe mambobinta, IPOB ta yi babban gargadi ga gwamnati
A wani labarin, A harin da 'Yan bindiga suka kai Cocin Haske Baptist da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane takwas yayin da suka sace wasu masu bauta da yawa.
Sai dai, ba a tantance adadin wadanda aka sace ba, sun kuma samu raunuka daban-daban tare da wani likita, Zakariah Dogo Yaro na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu yayin lamarin.
Cocin, wanda ke kauyen Manini Tasha, Kuriga Ward na karamar hukumar ta Chikun, maharan dauke da muggan makamai sun kai masa hari da misalin karfe 9 na safiyar Lahadi.
Asali: Legit.ng