An Tsinci Gawar Wani Yaron da Aka Sace a Magudanar Ruwa Bayan Biyan Fansa
- Wani makwabci ya hada kai da wasu sun sace wani yaro, kuma suka hallaka shi bayan karbar kudin fansa
- An rwauito cewa, bayan karbar kudin fansar Naira miliyan 5, masu garkuwar sun jefar da gawar yaron
- Mazauna yankin sun tabbatar da cewa, yaron ya gane masu garkuwar ne wannan yasa suka hallakashi
An tsinci gawar wani yaro da aka sace daga gidan iyayensa a wata unguwa da ke cikin garin Kaduna, kwanaki bakwai bayan an sace shi kuma aka ba da fansar Naira miliyan 5 don sakinsa.
Muhammad Kabir, da aka kashe, wanda aka dauke shi daga garin Badarawa da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, an yi imanin cewa masu garkuwar sun kashe shi.
An tsinci gawarsa a cikin magudanan ruwa a Kano bayan an kwashe mako guda ana bincike.
Majiyoyi daga yankin sun yi amannar cewa wani makwabci ne ya hada kai da wani mazaunin garin, wanda tsohon sojan ne, don sace yaron.
'Yan sanda sun cafke mutane uku, ciki har da makwabcin da aka ambata, bisa laifin yin garkuwa da kisan Kabir.
KU KARANTA: Boko Haram: Shekau Ya Sheke Wani Babban Kwandansa, Ya Nada Sabon Kwamanda
Majiyoyi sun kuma shaida wa jaridar Daily Trust cewa nan take da aka bayyana cewa yaron ya bata, an yi ta nemansa kwanaki kafin kira ya zo daga masu satar mutanen suna neman N50m, sannan daga baya suka rage kudin zuwa N35m kafin daga karshe suka amince kan N5m.
Abdulrahman Kabir Magayaki, dan uwa ga mamacin, ya shaida cewa an dauke marigayi Kabir daga gidansu zuwa Zariya daga nan zuwa Jihar Kano inda aka gano gawarsa bayan an biya kudin fansa.
“Daya daga cikin wadanda ake zargin sun dauki yaron makwabcinmu ne kuma tsohon sojan ne mazaunin yankin. Sun dauke shi zuwa Zariya daga nan zuwa Kano inda aka samo gawarsa a cikin magudanan ruwa bayan sun amshi kudin fansa na naira miliyan 5,” inji shi.
Ya ce an dawo da gawar wanda aka kashe zuwa Kaduna kuma an binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a ranar Asabar.
Wani mazaunin yankin ya ce tabbas an kashe yaron ne saboda ya fahimci fuskokin wadanda suka sace shi tunda duk suna zaune a yanki guda.
Cikakkun bayanai kan yadda aka kamo wadanda ake zargin suna nan a rubuce kuma sun jagoranci 'yan sanda zuwa inda aka jefar da gawar.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce wadanda ake zargin su uku sun amsa aikata laifin,.
Amma Jalige ya ce ba zai iya yin bayani kan asalin kasancewar daya daga cikin wadanda ake zargin soja ne ba har sai an kammala bincike.
KU KARANTA: Ku Kare Kanku Daga Harin ’Yan Bindiga, Gwamna Matawalle Ga ’Yan Zamfara
A wani labarin, An kama wasu ma'aikatan gwamnati da aikata fashi da makami a Zamfara, a cewar Gwamnatin Jihar, Channels Tv ta ruwaito.
A cewar wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Magaji Dosara ya sanya wa hannu a ranar Laraba, ma'aikatan gwamnatin suna daga cikin 35 da aka kama kuma ake zargin 'yan bindiga ne a Gusau, babban birnin jihar.
"Abin mamaki ne cewa, duk wadanda ake zargin 35 an kama su ne a Gusau, babban birnin jihar kuma wasu daga cikinsu ma'aikatan gwamnati ne," in ji sanarwar.
Asali: Legit.ng