Kwararre Ya Bayyana Dalilai 5 da Suka Sa Najeriya Ta Kasa Magance Matsalar Tsaro
- Matsalar rashin tsaro a Najeriya na ci gaba da mamaye kanun labarai a kafafen yada labaran Najeriya
- ‘Yan Najeriya da dama na ta bayyana ra’ayoyin su game da batun don taimakawa gwamnati wajen magance matsalar
- Wani masani kan nazarin bayanai ya lissafo hanyoyin da gwamnati a dukkan matakai zasu iya bi don magance matsalolin
Wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum kuma dan jarida, Rotimi Sankore ya yi bayani a shafinsa na Twitter don bayyana dalilan da ya sa gwamnatocin Najeriya a dukkan matakai suka kasa magance matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da zama ruwan dare a kasar.
Sankore yana mayar da martani ne ga kiraye-kirayen da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi inda ya bukaci Amurka da ta maida hedkwatarta na tsaro na Afirka daga Jamus zuwa nahiyar Afirka.
Sankore, mai gabatar da sanannen shirin gidan rediyo, Public Square Nigeria akan mita 99.3 tashar Nigeria Info FM, ya lissafo manyan dalilai guda biyar da yasa hukumomi ke gazawa wajen shawo kan matsalolin da suka addabi kasar.
KU KARANTA: An Tsinci Gawar Wani Yaron da Aka Sace a Magudanar Ruwa Bayan Biyan Fansa
A cewarsa, Najeriya ta kasa magance matsalolinta ne saboda:
1. 'Yan bindiga da masu tsattsauran ra'ayi suna da dumbin ma'aikata
2. 'Yan kasar miliyan 100 suna cikin tsananin talauci
3. 'Yan kasar miliyan 60 ba su iya karatu ko rubutu ba
4. Yara miliyan 10 zuwa 13 ba sa zuwa makaranta
5. Rashin aikin yi ya haura 33%
A sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa don tabbatar da cewa arewacin Najeriya ta kubuta daga ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, dole ne gwamnatoci su tabbatar da 'yancin dukkan 'yan mata na akalla halartar karatun firamare da sakandare zuwa shekaru 18).
Ya ci gaba da cewa auren dole ga yara, yawan haihuwa (yara 12 zuwa 32 ga mutum daya), da kuma rashin ci gaban karkara su ne manyan abubuwan da ke samar da karfi ga 'yan bindiga da masu tsattsauran ra'ayi.
Ya kuma bayyana cewa tsarin tsaro na Najeriya ya ruguje saboda shugabanci da tsarukan ci gaba sun durkushe.
KU KARANTA: Idan Ba Za Ka Iya Ba Ka Ba da Wuri, ECWA Ta Bukaci Buhari Ya Yi Murabus
A wani labarin, Kungiyar kwadago reshen jihar Kaduna (TUC) ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta biya hakkokin dukkan wadanda suka yi ritaya da kuma ma’aikatan da lamarin kora ya shafa kwanan nan.
Kungiyar kwadagon ta ce biyan zai magance matsin tattalin arzikin da suke fama dashi da kuma rage radadin rashin ayyukan yi, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar na jihar, Kwamared Abdullahi Danfulani da ya bayyana hakan a wani taron manema labarai don bikin ranar ma’aikata, ya ce yana da matukar ciwo a sallami mutum daga aiki ko kuma ya yi ritaya daga aiki ba tare da an biya shi hakkokinsa ba.
Asali: Legit.ng