Ina da Kwarin Gwiwa Najeriya Za Ta Shawo Kan Matsalolinta, in ji Obasanjo
- Obasanjo ya bayyana kwarin gwiwarsa game da Najeriya wajen kawo karshen matsalolin da take fuskanta
- A cewarsa, shi mutum ne mai kwarin gwiwa a kan Najeriya, kuma za ta shawo kan matsalolinta
- Sai dai, duba da yanayin tsaron kasar, majalisa ta bukaci shugaba Buhari ya ayyana dokar ta baci a fannin tsaro
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana yakinin cewa Najeriya za ta shawo kan matsalolin tsaro da sauran matsalolin da take fama da su a yanzu, Channels Tv ta ruwaito.
Ya ce duk da cewa kira ga rabuwar kasar na iya zama da karfi, ba za a taba jinsa ba kuma zai zama tarihi nan gaba.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin wani taro a jihar Ogun inda gwamna Dapo Abiodun da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, su ma suka yi kira ga zaman lafiya, hadin kai, da kawo karshen tashin tashina a kasar.
"'Yan uwana biyu sun yi magana game da halin da muke ciki," in ji shi yayin da yake magana kan gwamnonin biyu da suka yi magana a taron.
KU KARANTA: Shehu Sani Ya Caccaki Kiran da Buhari Ya Yi Na Gayyato Amurka Zuwa Afrika
Obasanjo ya kara da cewa, "Ku sani, ni mutum ne mai kwarin gwiwa game da abubuwa da dama, musamman ma game da Najeriya."
Da yake magana cikin yaren Yarbanci, dattijon ya bada wani misali da yake nuna cewa duk da halin da ake ciki yanzu, tabbas kasar za ta ci nasara.
A yayin da ake ci gaba da nuna damuwa game da rashin tsaro a kasar, mambobin majalisar wakilai sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana dokar ta-baci a kan tsaro don hanzarta bin dukkan hanyoyin da za a bi don farfado da zaman lafiya a kasar.
Sun kuma umarci Kwamitocin Tsaro na Majalisar da su fara binciken kwakwaf kan dukkan sojoji da kayayyakin tsaro da makamai kuma su bada rahoto cikin makonni hudu.
'Yan majalisar sun yi Allah wadai da hare-haren da aka kaiwa jami'an tsaro da cibiyoyi da sassan kasar kuma sun jajanta wa danginsu, da kuma iyalai da al'ummomin da suka fuskanci hari na 'yan bindiga da ta'addanci, da ayyukan 'yan ta'adda.
KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana
Ta ce ta bukaci manyan hafsoshin tsaron kasar su gaggauta tura sojoji domin kare iyakokin yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.
Majalisar ta yanke wannan shawarar ce bayan zamanta na ranar Talata wanda a ciki 'yan majalisar suka bayyana damuwa game da halin da tsaro yake ciki a kasar.
Asali: Legit.ng