Babu Shugaban da Zai So Kasarsa Ta Lalace, Ku Dai Ku Hada Kai, Tinubu Ga ’Yan Najeriya

Babu Shugaban da Zai So Kasarsa Ta Lalace, Ku Dai Ku Hada Kai, Tinubu Ga ’Yan Najeriya

- Shugaban jam'iyyar APC ta kasa ya nemi 'yan Najeriya da su hada kai don magance matsalolin kasar

- Ya ce kowace kasa dole ta fuskanci irin wadannan matsaloli kafin daga baya ta samu ci gaba mai dorewa

- Ya kuma bayyana cewa, babu shugaban da zai so kasar ta rufta cikin halin rikici yana ji yana kallo

Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya ce Najeriya na bukatar hadin kai don shawo kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a yanzu, TheCbale ta ruwaito.

Da yake magana a ranar Litinin da yamma bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari tare da Bisi Akande; tsohon shugaban riko na APC, Tinubu ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da aiki don ci gaban kasar.

Ya kara da cewa babu wani shugaban kasa da ke son kasarsa ta fada rikici, yana mai bayanin cewa hada karfi da karfe ne kawai zai kawo karshen kalubalen tsaro.

KU KARANTA: An Kwamushe Masu Bai Wa ’Yan Boko Haram Bayanai, Ciki Har da Likita a Jihar Neja

Babu Shugaban da Zai So Kasarsa Ta Lalace, Ku Dai Ku Hada Kai, Tinubu Ga ’Yan Najeriya
Babu Shugaban da Zai So Kasarsa Ta Lalace, Ku Dai Ku Hada Kai, Tinubu Ga ’Yan Najeriya Hoto: freedomradionig.com
Asali: UGC

“Hanya mafi kyau ita ce abin da muke yi; haduwa wuri guda don rage bindiganci, don matsawa ga hadin kai da kuma iya inganta kyakkyawar Najeriya ga mutane.

"Walwalar mutanenmu yana da matukar muhimmanci. Kuma tabbas, kowace al'umma dole za ta ratsa cikin wadannan matsaloli da mawuyacin lokaci.

"Ta yaya muke sadar da shi ga mutane, wadanne fannoni ne za su taimaka wajen saukaka wa mutane lamarin cikin sauki, wadannan sune ra'ayoyi kan yadda za a iya sauya shugabancin kasar," in ji shi.

“Babu wani shugaban kasar da zai so kasarsa cikin rudani. Shin kun taba gabi? Ku nuna min daya. Babu wani wanda zai so 'yan kasarsa su shiga cikin matsalar 'yan ta'adda da hadari.

"Babu wani shugaba ko mai mulki da zai so al’ummarsa ta wargaje ta hanyar kabilanci, bambancin addini da duk irin wadannan..."

KU KARANTA: Majalisar Dattawa Ta Nemi Ganawa da Shugaba Buhari Cikin Gaggawa kan Matsalar Tsaro

A wani labarin, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa Najeriya za ta iya shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar kasar nan, yana mai bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na sake fasalta dukkan tsarin tsaro a kasar.

Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin da ya karbi ziyarar ban girma a fadar shugaban kasa ta mai martaba, Yakanaje Uke, (na jihar Nasarawa), Alhaji Dr. Ahmed Abdullahi Hassan, TVC ta ruwaito.

A cewar Mataimakin Shugaban kasar, “babu wata shakka ko kadan cewa muna fuskantar kalubalen tsaro, amma muna iya shawo kansu. Matsayin jagoranci shine a zauna a yi tunani kan matsalolin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.