An Bukaci Jihohi 26 Su Shirya saboda Fargabar Ambaliyar Ruwa a 2026

An Bukaci Jihohi 26 Su Shirya saboda Fargabar Ambaliyar Ruwa a 2026

  • Ma’aikatar muhalli ta ƙasa ta yi gargaɗi kan yiwuwar faruwar ambaliyar ruwa mai muni tsakanin ranakun 22 ga Yuni zuwa 5 ga Yulin 2026
  • Ta bayyana cewa jihohi 26 da babban birnin tarayya Abuja na cikin yankunan da da za su iya fuskantar babbar ambaliya idan hasashen ya tabbata
  • Ma'aikatar ta ayyana yankuna da dama a faɗin Najeriya da ya kamata su zauna a cikin shiri kuma su dauki matakan da suka dace tun da wuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ma’aikatar muhalli ta tarayya ta yi gargaɗin cewa aƙalla jihohi 26 da Abuja na iya fuskantar ambaliya tsakanin 22 ga Yuni zuwa 5 ga Yuli, 2026.

Ma'aikatar ta sanar da cewa za a iya samun ambaliyar ne sakamakon hasashen ruwan sama mai ƙarfi a sassan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Andy Burnham: 'Dan siyasar da ake hasashen zai zama Firayim Ministan Birtaniya

Yadda aka yi amabaliyar ruwa
Mutane na tafiya yayin ambaliyar ruwa a Yobe a 2025. Hoto; Getty Images
Source: Getty Images

A cikin hasashen ambaliya da ta fitar a ranar Litinin, Punch ta rahoto cewa ma’aikatar ta bayyana ɗaruruwan al’ummomi a faɗin ƙasar a matsayin yankunan da ke cikin haɗari.

Jihohin da ake hasashen ambaliya

Jihohin da aka sanya a rukuni mai hadari sosai sun haɗa da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Kwara, Legas, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo da Ribas.

Wasu daga cikin yankunan da aka bayyana sun haɗa da Aba, Arochukwu da Umuahia a jihar Abia; Jimeta da Numan a Adamawa; Eket, Oron da Uyo a Akwa Ibom; Onitsha da hanyoyin magudanan ruwa na Awka a Anambra; da Yenagoa, Brass da garin Nembe a Bayelsa.

Ma’aikatar ta kuma sanya Makurdi, Gboko da Katsina-Ala a Benue; Calabar da Creek Town a Cross River; Asaba, Warri da Sapele a Delta; da Abakaliki, Afikpo da Onueke a Ebonyi cikin yankunan da ke cikin haɗari.

Kara karanta wannan

Roko na musamman da Sarki Sanusi II ya yi ga kungiyar EU game da Kano

Wuraren da za a yi ambaliya

Sauran wuraren da aka lissafa sun haɗa da tsakiyar Benin City da Auchi a Edo; Ado-Ekiti da Ikere-Ekiti a Ekiti; Enugu, Nsukka da garin Oji River a Enugu; Owerri, Orlu da Okigwe a Imo.

Haka zalika akwai Lokoja da Ajaokuta a Kogi; Ilorin, Jebba da Pategi a Kwara; da al’ummomi da dama a jihar Legas ciki har da Agege, Alimosho, Apapa, Badagry, Ikeja, Ikorodu, Lagos Island, Lekki da Surulere.

A jihar Neja, ma’aikatar ta bayyana Bida, Minna, Mokwa, Suleja da Kontagora a matsayin wuraren da ke cikin haɗari, yayin da Abeokuta, Ota da Sagamu suka kasance cikin jerin wuraren da ke cikin haɗari a Ogun.

Gidaje sun rushe bayan ambaliyar ruwa
Wasu gidaje da suka ruguje yayin ambaliya a Yobe a 2025. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Karin wuraren da gargadin ya shafa

Gargaɗin ya shafi Akure, Owo da Okitipupa a Ondo; Oshogbo, Ile-Ife da Ilesa a Osun; Ibadan, Ogbomoso da Oyo a Oyo; da tsakiyar Port Harcourt, Bonny, Ahoada da Omoku a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shari'ar daruruwan wasu da ake zargi da ta'addanci

Ma’aikatar ta kuma sanya wasu sassan Adamawa, Babban Birnin Tarayya, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Filato da Taraba a cikin rukunin yankunan da ke cikin babban haɗarin ambaliya.

Daga cikin al’ummomin da aka sanya a wannan rukuni akwai Yola ta Arewa, Yola ta Kudu, Mubi da Gurin a Adamawa; Abuja Municipal, Gwagwalada, Kubwa, Nyanya da Wuse a Babban Birnin Tarayya; Birnin Kebbi da Argungu a Kebbi; Bako a Kogi; da Keffi, Lafia, Karu da Toto a Nasarawa.

Sauran sun haɗa da Jos da Jos ta Arewa a Filato, da Jalingo, Wukari, Takum, Serti da Karim Lamido a Taraba.

Jihohin da za a fi samun ruwa

A wani labarin, mun rahoto muku cewa hukumar NiMet ta yi hasashen jihohin da za a fi samun ruwan sama a damunar shekar 2026.

Hukumar hasashen yanayin ta lissafa Kebbi, Kaduna, Gombe Taraba, Benue a cikin jihohin Najeriya da za su samu ruwa sosai a bana.

Biyo bayan hasashen, NiMet ta bukaci manoma da sauran masu ruwa da tsaki su dauki matakan da suka dace yayin da damu ke kankama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng