Majalisar Dattawa Ta Nemi Ganawa da Shugaba Buhari Cikin Gaggawa kan Matsalar Tsaro

Majalisar Dattawa Ta Nemi Ganawa da Shugaba Buhari Cikin Gaggawa kan Matsalar Tsaro

- Majalisar dattawa a Najeriya ta bayyana bukatar ganin shugaba Muhammadu Buhari cikin gaggawa

- Majalisar ta kuma bukaci a dasa rundunonin soji a bangarori da dama na kasar da ke fama da rashin tsaro

- Manufar ganawa da shugaban in ji majalisar shine samar da mafita mai dorewa ga matsalolin tsaron kasar

Majalisar dattawa ta ce za ta nemi ta zauna da shugaba Muhammadu Buhari a madadin sanatoci 109 saboda halin da ƙasar ke ciki na matsalar tsaro, BBC Hausa ta ruwaito.

Ta ce ta bukaci manyan hafsoshin tsaron kasar su gaggauta tura sojoji domin kare iyakokin yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.

Majalisar ta yanke wannan shawarar ce bayan zamanta na ranar Talata wanda a ciki 'yan majalisar suka bayyana damuwa game da halin da tsaro yake ciki a kasar.

KU KARANTA: An Yi Bata-Kashi Tsakanin Sojojin Chadi Da ’Yan Ta’adda, an Kashe Soji 12

Majalisar Dattawa Ta Nemi Ganawa da Shugaba Buhari Cikin Gaggawa kan Matsalar Tsaro
Majalisar Dattawa Ta Nemi Ganawa da Shugaba Buhari Cikin Gaggawa kan Matsalar Tsaro Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar majalisar, akwai bukatar a hanzarta kafa sansanin sojoji da na yan sanda na din-din-din a kusa da kananan hukumomin Shiroro da Rafi da ke jihar Neja.

Kafin majalisar ta dauki wannan matakin, Sanata Olubunmi Adetunmbi ya ce la'akari da karuwar hare-hare a sassan kasar, akwai bukatar a yi ganawar sirri da shugaba Muhammadu Buhari domin samar da mafita mai dorewa game da lamarin da ya zama abin kunya.

KU KARANTA: An Nada Wanda Idriss Deby Taba Kora a Matsayin Sabon Firaministan Chadi

A wani labarin, ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun yi zama inda su ka tattauna a game da matsalar tsaro da ake fama da ita a garuruwa da-dama na kasar nan a halin yanzu.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto dazu cewa majalisar tarayyar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa dokar ta-baci a kan sha’anin tsaro.

Majalisar wakilan ta na ganin cewa hakan ne zai sa a iya kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel