Saudiyya Ta Fara Rabon Tallafin Abinci a Najeriya, An Ji Wadanda Za Su Amfana
- Kasar Saudiyya ta fara rabon tallafin kayan abinci ga mutane masu karamin karfi sama da 145,000 da suka fito daga jihohi biyar na Najeriya
- Shirin tallafin abincin ya kunshi kwaryar abinci 24,302 da za a raba wa iyalai mabukata, wadda ke dauke da shinkafa, man girki da sauran su
- Rahoto ya nuna cewa za a raba wannan tallafin ne ga 'yan gudun hijira da al'ummomin da 'yanrikice-rikicen 'yan tada kayar baya ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Yobe - Ƙasar Saudiyya ta fara raba tallafin abinci ga al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali a Najeriya ƙarƙashin shirin tallafin abinci na shekarar 2026.
A karkashin shirin, ana sa ran sama da mutane 145,000 za su amfana a jihohi biyar da matsalolin gudun hijira, rashin tsaro da sauran ƙalubalen jin ƙai suka shafa.

Source: Twitter
Saudiyya ta kawo tallafin abinci a Najeriya
An ƙaddamar da shirin ne ta ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja tare da haɗin gwiwar Cibiyar Taimakon Jin Ƙai da Agaji ta Sarki Salman (KSrelief) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), in ji rahoton Tribune.
Rahoton ya nuna cewa shirin zai samar da kwaryar abinci guda 24,302 da za a raba wa gidajen da ke buƙatar taimako.
A cewar sanarwar ma’aikatar yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ta tarayya a ranar Litinin, kowace kwarya tana da nauyin kusan kilo 60, kuma ta ƙunshi muhimman kayan abinci kamar shinkafa, man girki, wake, gishiri da sauran kayan masarufi.
Sanarwar ta bayyana cewa darajar tallafin ya haura dala miliyan 1.5, kuma zai amfani mutane 145,812 a faɗin Najeriya.
Jihohin da za a raba tallafin
Da yake magana yayin bikin fara shirin a Damaturu, Darakta Janar na NEMA ya sake tabbatar da aniyar hukumar wajen tabbatar da “rarraba kayan abincin cikin gaskiya da inganci ga waɗanda aka tantance za su amfana”, bisa aikin hukumar na kula da agajin gaggawa da tallafin jin ƙai a Najeriya.
Rahoton ya nuna cewa za a raba kayan abincin ne a jihohi biyar da suka haɗa da Yobe, Benue, Anambra, Kebbi da Taraba.
Ma’aikatar ta ce wannan shiri na nuna ci gaba da goyon bayan Saudiyya ga al’ummomin da ke da buƙatar dauki kan tattalin arziki a Najeriya da kuma yankin Tafkin Chadi.
Sanarwar da aka wallafa a shafin hukumar na X ta ce:
“Wannan shiri ya nuna ci gaba da jajircewar Masarautar Saudiyya wajen bayar da taimakon jin ƙai da tallafa wa al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali a Najeriya da yankin Tafkin Chadi."

Source: Twitter
Hadin gwiwar Najeriya da Saudiyya
Ta ƙara da cewa ta hannun KSrelief, Saudiyya ta ci gaba da samar da muhimman tallafin agaji domin inganta samar da abinci da rage wahalhalun mutanen da rikice-rikice suka shafa.
Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwar NEMA da KSrelief wajen magance matsalolin jin ƙai da ke addabar al’umma a faɗin ƙasar.
“Haɗin gwiwar NEMA da KSrelief na nuna muhimmancin haɗin kan ƙasa da ƙasa wajen magance ƙalubalen jin ƙai da tallafa wa al’ummomin da ke buƙata."
- Ma'aikatar yada labarai.
Saudiyya ta gwangwaje Kano, Abuja
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, gwamnatin kasar Saundiyya ta bai wa Najeriya tallafin dabino tan 100 domin rabawa mabuƙata.
Jakadan Saudiyya a Najeriya Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi ya ce tallafin za a raba shi ne tsakanin babban brnin tarayya Abuja da jihar Kano.
Wannan tallafi wani ɓangare ne na shirye-shiryen agaji da jin ƙai da Saudiyya ke gudanarwa domin taimaka wa al’ummar musulmi da sauran mabukata a faɗin duniya.
Asali: Legit.ng


