An Ga Tsohon Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa, Okowa a Ofishin Hukumar EFCC
- Tsohon gwamnan Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, ya kai ziyara ofishin EFCC da ke Legas yayin da ake ci gaba da bincike kan zargin karkatar da Naira tiriliyan 1.3
- Rahotanni sun ce tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasar ya je ne domin neman a maido masa fasfo dinsa na tafiya kasashen waje
- EFCC na zarginsa da karkatar da kudaden 13% na rabon mai da kuma sayen kadarori da kudaden gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Sanata Ifeanyi Okowa, ya kai ziyara ofishin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ke Ikoyi a Legas.
Wannan ziyara da Okowa ya kai na zuwa ne yayin da hukumar EFCC ke ci gaba da bincike kan zargin karkatar da Naira tiriliyan 1.3 na kudaden gwamnatin Delta a lokacin mulkinsa.

Source: Facebook
Majiyoyi daga hukumar sun shaida wa Leadership cewa ziyarar Okowa na da nasaba da binciken kudaden kaso 13 na jihohi masu arzikin fetur wanda Delta ta karba tsakanin 2015 zuwa 2023.
Hukumar EFCC ta taba kama shi a 2024
A ranar 4 ga Nuwamban 2024 ne EFCC ta kama Okowa tare da tsare shi domin yi masa tambayoyi a ofishinta na shiyyar Fatakwal kan wannan batu.
Rahotanni sun nuna cewa babban dalilin ziyararsa ta baya-bayan nan shi ne neman a mayar masa da fasfo dinsa na kasa da kasa.
An ce ya shaida wa masu bincike cewa yana bukatar tafiya kasashen waje domin neman kulawar lafiya cikin gaggawa.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a tabbatar ko EFCC ta amince da bukatarsa ko ta mayar masa da fasfon ba.
Ana zarginsa da karkatar da kudade
A watan Nuwamban 2024, EFCC ta bayyana cewa tana binciken Okowa kan zargin karkatar da Naira tiriliyan 1.3 a lokacin da ya yi shekaru takwas yana gwamnan jihar Delta.
Haka kuma ana zarginsa da amfani da kudaden gwamnati wajen sayen kadarori a Asaba, babban birnin jihar Delta, da kuma Abuja.
Okowa ya musanta aikata laifi
Da yake magana bayan kama shi a wancan lokaci, Okowa ya ce an yi amfani da kudaden jihar yadda ya kamata a lokacin mulkinsa.
Ya kuma bayyana cewa bai damu da binciken da ake yi masa ba, yana mai cewa ba ya tsoron a bincike shi.
“Duk abin da ke faruwa, ban damu ba. Na fada a baya cewa ban tsoron a bincike ni,” in ji Okowa.

Source: Twitter
A watan Afrilun 2025, Okowa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC tare da magajinsa, Gwamna Sheriff Oborevwori, da wasu manyan yan siyasa a jihar Delta.
EFCC ta tsare shugaban hukumar ECN
A wani labarin, kun ji cewa jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, sun tsare shugaban hukumar makamashi ta Najeriya (ECN), Mustapha Abdullahi.
Majiyoyi daga EFCC sun bayyana cewa zargin da ake yi wa shugaban na hukumar makamashi ta Najeriya ya shafi kudade wanda adadinsu ya kai N500bn.
An naɗa Mustapha Abdullahi ne a matsayin shugaban ECN bayan ya shafe shekaru fiye da 10 yana aiki a hukumar NUPRC ta Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

