Gwamnatin Kogi Tayi Cikakken Bayani Kan Kisan da Yan Bindiga Suka Yiwa Kwamishinanta

Gwamnatin Kogi Tayi Cikakken Bayani Kan Kisan da Yan Bindiga Suka Yiwa Kwamishinanta

- Gwamnatin jihar Kogi tayi jawabi a kan harin da aka kaima kwamishinan ta da kuma wani shugaban ƙaramar hukuma

- Gwamnatin ta tabbatar da kai harin, inda ta bayyana cewa kwamishinan hukumar fansho ya rasa ransa a harin, kuma an yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta yamma

- Kwamishinan yaɗa labaran jihar ne ya bayyana haka, yace har yanzun ba'a gano inda yan bindigan suka kai shugaban ƙaramar hukumar ba

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da cewa yan bindiga sun kashe kwamishinan hukumar fansho ta jihar, Solomon Adebayo, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Jagoran APC Bola Tinubu Yayi Zazzafan Martani Ga Masu Son Ɓallewa Daga Najeriya

A wani jawabi da gwamnatin ta fitar ta bakin kwamishinan yaɗa labarai, Kingsley Fanwo, yace marigayin ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake dawowa daga Jihar Kwara tare da shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta yamma, Pius Kolawole.

Ya ƙara da cewa duk da kasancewar yan bindigar hari kawai suka kaiwa ma'aikatan, amma sai da suka tafi da shugaban ƙaramar hukumar.

Gwamnatin Kogi Tayi Cikakken Bayani Kan Kisan da Yan Bindiga Suka Yiwa Kwamishinanta
Gwamnatin Kogi Tayi Cikakken Bayani Kan Kisan da Yan Bindiga Suka Yiwa Kwamishinanta Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Kuma sun nemi iyalanshi da su biya kuɗin fansa kimanin 100 miliyan kafin su sake shi.

Yace: "Muna tabbatar wa mutane cewa yan bindiga sun kai wani mummunan hari a kusa da Eruku, ƙaramar hukumar Ekiti jihar Kwara. Hon. Adebayo ya rasa ransa sakamakon harbin da aka masa."

KARANTA ANAN: Salon Mulkin Buhari Ne Zai Tarwatsa Najeriya, Tsohuwar Minista Ta Caccaki DSS

"Har yanzun ba'a san inda shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta yamma yake ba, amma hukumomin tsaro na jihohin Kwara da Kogi suna aiki matuƙa domin ganin shugaban ya dawo cikin ƙoshin lafiya."

Kwamishinan ya ƙara jaddada wa mutanen jihar cewa gwamnati zata magance duk wasu yan ta'adda dake jihar.

Ya kuma ce gwamnatin Yahaya Bello ba zata bar komai ba har sai ta tabbatar da jihar Kogi tafi kowacce jiha zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.

Yayin da yake gargaɗin mutane da su guji ƙirƙirar jita-jita da zata ƙara gurɓata tsaron jihar, Kakakin gwamnatin yayi kira ga yan Najeriya da su baiwa gwamnati haɗin kai wajen daƙile ƙalubalen tsaro.

A wani labarin kuma Ku Kawar da Mulkin APC Idan Baku Gamsu Ba Da Shi Ba, Gwamnan APC Ya Baiwa Matasa Shawara

Shekaru kaɗan suka rage babban zaɓen 2023 ya iso amma gwamna Fayemi ya shawarci matasa su fara aiki tun kafin zuwan zaɓen.

Gwamnan Ekiti yace maimakon damuwa da yawan ƙorafi, duk wadanda basa goyon bayan mulkin APC zasu iya haɗa kansu su kawar da ita a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel