Wasu Kasurguman 'Yan Bindiga Sun Sheke Wani Kwamishanin Hukumar Fansho

Wasu Kasurguman 'Yan Bindiga Sun Sheke Wani Kwamishanin Hukumar Fansho

- Wasu 'yan bindiga da ba san ko su waye ba sun hallaka kwamishinan hukumar Fansho a jihar Kogi a jiya Asabar

- An ruwaito cewa, sun yi harbi ba kakkautawa kan motar kwamishinan na Fansho a yayin harin

- Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta kuma bayyana cewa ana kan bincike

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun hallaka kwamishinan hukumar fansho na jihar Kogi, Solomon Akeweje, jaridar Punch ta ruwaito.

An rahoto cewa an kashe shi ne da yammacin ranar Asabar yayin da yake dawowa daga Ilorin zuwa Kabba.

An ce 'yan bindigan sun harbi motarsa a Eruku, tazarar kilomita kadan daga Egbe a jihar.

KU KARANTA: Kwararre Ya Bayyana Dalilai 5 da Suka Sa Najeriya Ta Kasa Magance Matsalar Tsaro

'Yan Bindiga Sun Sheke Wani Kwamishanin Hukumar Fansho a Wata Jiha
'Yan Bindiga Sun Sheke Wani Kwamishanin Hukumar Fansho a Wata Jiha Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Har yanzu ba a san inda Shugaban Karamar Hukumar Yagba ta Yamma, Pius Kolawole yake ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoton, kasancewar suna tare da Akeweje lokacin da lamarin ya faru yake ba.

An gano cewa Kwamishinan Hukumar ta Fansho ya mutu ne bayan harsasai sun same shi.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ayuba Ede, ya ce "lamarin ya faru ne a Eruku general area na jihar Kwara ".

Ya ce ana kuma ci gaba da bincike kan lamarin.

KU KARANTA: An Kama Wasu Ma’aikatan Gwamnati Daga Cikin ’Yan Bindiga a Jihar Zamfara

A wani labarin, An tsinci gawar wani yaro da aka sace daga gidan iyayensa a wata unguwa da ke cikin garin Kaduna, kwanaki bakwai bayan an sace shi kuma aka ba da fansar Naira miliyan 5 don sakinsa.

Muhammad Kabir, da aka kashe, wanda aka dauke shi daga garin Badarawa da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, an yi imanin cewa masu garkuwar sun kashe shi.

An tsinci gawarsa a cikin magudanan ruwa a Kano bayan an kwashe mako guda ana bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.