Da Ɗuminsa: Yan Bindiga sun kai hari Zariya, Sun yi Awon gaba da mata da Yara

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga sun kai hari Zariya, Sun yi Awon gaba da mata da Yara

- Wasu yan bindiga sun farmaki wata unguwa a ƙaramar hukumar Zariya dake jihar Kaduna, sun yi awon gaba da mata

- Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigar sun isa unguwar ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare inda suka fara bincike gida-gida don samun waɗanda zasu sace

- Mai magana da yawun yan sandan jihar Kaduna ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma tabbatar da cewa jami'an yan sanda na cigaba da gudanar da bincike

Wasu yan bindiga sun kai hari a wata unguwa dake cikin garin Zariya, jihar Kaduna, sun sace mata daga ciki har da wata mai juna biyu.

Wata majiya ta faɗawa jaridar Daily Nigerian cewa yan bindigar sun kai hari unguwar 'Low-cost' da misalin ƙarfe 9:30 na dare ranar Lahadi.

KARANTA ANAN: NAF ta bayyana Matakin da zata ɗauka kan zargin da ake mata na kai hari ta sama kan sojoji a Mainok

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun ci karen su ba babbaka har na tsawon awanni huɗu kafin jami'an tsaro su ƙaraso yankin.

Majiyar tace yan bindigar sun shiga gida-gida suna binciken waɗanda zasu sace amma dai basuyi nasara ba.

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga sun kai hari Zariya, Sun yi Awon gaba da mata da Yara
Da Ɗuminsa: Yan Bindiga sun kai hari Zariya, Sun yi Awon gaba da mata da Yara Hoto: theangleonline.com.ng
Asali: UGC

Majiyar tace:

"Yan bindigar ba suyi nasara ba, saboda mafi yawancin mazan unguwar sun tafi sallar tarawihi, wasu kuma basu dawo daga wajen aikinsu ba. Daga nan sai suka yanke hukuncin ɗaukar mata da kuma yara."

"Sun harbi mutane huɗu, waɗanda a yanzun haka suna asibitin Sawaba suna karɓar kulawa ta musamman."

Wani rahoto ya bayyana cewa an samu nasarar kama mutane uku daga cikin waɗanda suka kai harin.

Kakakin yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya tabbatar da kai harin, ya ce mutum huɗu kacal suka samu nasarar sacewa.

KARANTA ANAN: Sanata Ali Ndume ya faɗawa gwamnatin tarayya matakin da yakamata ta ɗauka kan masu ɗaukar Nauyin Boko Haram

Mr. Jalige yace yanzun haka yan sanda na cigaba da bincike kan lamarin da zammar kuɓutar da waɗanda aka sace ɗin a raye.

Sai-dai, mijin ɗaya daga cikin matan da aka sace, Haruna Sani, ya bayyanawa manema labarai cewa an kirashi da misalin ƙarfe 10:00 na daren Lahadi aka faɗa masa yan bindiga sun shiga gidan shi.

Sani yace nan take yayi gaggawar sanar da jami'an yan sanda, waɗanda suka ɗauki matakin gaggawa, kuma sukayi musayar wuta da yan bindigar na tsawon mintuna 25.

A wani labarin kuma Tsohon Sufetan Yan Sanda Ya Bayyana Hanyar da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro

Wani tssohon sufetan yan sandan ƙasar nan ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar yadda zata yi ta daƙile matsalar tsaron ƙasar nan da jami'an yan sanda kawai.

Ya ce babu isassun yan sanda a ƙasar nan idan ka kwatanta da yawan jama'ar da Najeriya ke dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel