'Yan Sanda Sun Bindige Dan Ta'adda Mai Garkuwa da Mutane

'Yan Sanda Sun Bindige Dan Ta'adda Mai Garkuwa da Mutane

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ta kashe wani da ake zargi mai garkuwa da mutane ne tare da kama wani da ake zato yana satar mutane a Edo
  • Rahoto ya nuna cewa an ƙwato mota, bindiga, harsasai biyu da tsabar kudi Naira miliyan 2.25 da kuma babur daga wajen wana aka kama
  • Biyo bayan lamarin, Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya bayyana shirin kafa kotu ta musamman domin shari'ar masu garkuwa da mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Rahotanni sun nuna cewa rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne.

Bayan kashe shi har lahira, 'yan sanda sun sanar da kama wani da ake dangantawa da sace wata mata a wata kasuwa da ke Benin City.

Kara karanta wannan

Da gaske yan ta'adda sun harbo jirgin sojojin sama a Niger? Bayanai sun fito

Taswirar jihar Edo
Taswirar jihar Edo a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Bayanin rundunar 'yan sanda

Punch ta wallafa cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Agbonika, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargi a hedikwatar rundunar da ke Benin City.

Agbonika ya ce jami’an sashen IRT, bisa sahihan bayanan sirri da suka samu, sun kama wani wanda ake zargi mai suna Marvelous Issac mai shekaru 32 da haihuwa, dangane da satar mutane.

A cewarsa, wani wanda ake zargi da satar mutane mai suna Precious, ya mutu bayan musayar wuta da jami’an ‘yan sanda.

“Bayan samun rahoton garkuwa da wata mata a Kasuwar Kayan Lambu da ke Benin City a ranar 14 ga Yuni, 2026, jami’an IRT a Edo, bisa sahihan bayanan sirri, sun samu nasarar kama Marvelous Issac mai shekaru 32, wanda aka gano yana cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane,”

In ji kwamishinan ‘yan sandan.

“Yayin gudanar da aikin, wani wanda ake zargi mai suna Precious ya mutu bayan musayar harbin bindiga da jami’an ‘yan sanda.”

Kara karanta wannan

Trump ya yi magana kan 'harin Amurka' da ya kashe yara 'yan makaranta 170 a Iran

Kayayyakin da aka kwato

Kwamishinan ya ce an ƙwato wata mota kirar Lexus RX 350 mai launin ja da lambar rajista EKP 848 AE, wadda ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin.

The Guardian ta wallafa cewa ta ƙara da cewa wanda aka kama ya amsa cewa an yi amfani da motar tare da bindiga da harsasai guda biyu aiwatar da garkuwa da mutumin.

Agbonika ya kuma bayyana cewa an ƙwato Naira miliyan 2.25 da ake zargin kuɗi kudin fansa ne da kuma babur, kuma za a yi farautar wadanda suka tsere.

Gwamna Monday Okpebholo
Gwamna Monday Okpebholo a wajen wani taro a Edo. Hoto: Monday Okpebholo
Source: Twitter

Gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya bayyana shirin kafa kotu ta musamman domin sauraron shari’o’in masu garkuwa da mutane da ‘yan ƙungiyoyin asiri domin tabbatar yanke hukunci cikin gaggawa.

Za a kama Bello Turji

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa sannu a hankali za su kama babban dan ta'adda, Bello Turji.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto mutanen da aka gani a bidiyo tare da Janar Rabe a hannun 'yan bindiga

Gwamna Dauda Lawal ya ce yana da tabbacin cewa za su kama dan ta'addan lura da muhimman matakan da suke dauka a fadin jihar Zamfara.

Ya kara da cewa babu wani dan ta'adda da ya gagari hukuma ko jami'an tsaro, inda ya ce sun kashe da dama daga cikin masu garkuwa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng