An Kama Wasu Ma’aikatan Gwamnati Daga Cikin ’Yan Bindiga a Jihar Zamfara

An Kama Wasu Ma’aikatan Gwamnati Daga Cikin ’Yan Bindiga a Jihar Zamfara

- Gwamnatin jihar Zamfara ta kame wasu bata-garin ma'aikatan gwamnati cikin 'yan bindiga

- Tuni jihar ta gudanar da bincike kuma ta tura su zuwa babban birnin tarayya Abuja don hukunci

- Hakazalika gwamnatin jihar ta gargadi masu ba da gidajensu haya ga masu aikata laifuka a jihar

An kama wasu ma'aikatan gwamnati da aikata fashi da makami a Zamfara, a cewar Gwamnatin Jihar, Channels Tv ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Magaji Dosara ya sanya wa hannu a ranar Laraba, ma'aikatan gwamnatin suna daga cikin 35 da aka kama kuma ake zargin 'yan bindiga ne a Gusau, babban birnin jihar.

"Abin mamaki ne cewa, duk wadanda ake zargin 35 an kama su ne a Gusau, babban birnin jihar kuma wasu daga cikinsu ma'aikatan gwamnati ne," in ji sanarwar.

"Don haka Gwamnatin Jiha ta nuna farin ciki kan kamun yan bindiga 35 da ke firgita mutane a cikin garin Gusau."

KU KARANTA: Buhari Bai da Damu da Halin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki Ba, PDP Ta Caccaki Buhari

An Kama Wasu Ma’aikatan Gwamnati Daga Cikin ’Yan Bindiga a Jihar Zamfara
An Kama Wasu Ma’aikatan Gwamnati Daga Cikin ’Yan Bindiga a Jihar Zamfara Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

“An riga an yi masu tambayoyi kuma sun amsa laifuffukansu daban-daban kuma tuni aka tura su Abuja don ci gaba da bincike kafin a hukunta su.”

Sanarwar ta ce "Don haka gwamnati ta gargadi 'yan bindiga da su yi watsi da aikata laifuka su rungumi tattaunawa da gwamnatin jihar da shirin samar da zaman lafiya don zama 'yan kasa na gari.

Hakazalika sanarwar ta "jaddada aniyar gwamnati na daukar matakan hukunta masu aikata laifuka, cikin gaggawa."

“Gwamnatin jihar ta kuma gargadi sarakunan gargajiyar da su sa ido sosai kan masu gidaje da ke ba da gidajensu ga mutanen da ke da hali maras kyau a cikin yankunansu.

A cewar gwamnati, "Nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fara kamo duk wani mai gidan da aka samu yana bayar da gidansa haya ga 'yan bindiga masu satar mutane, masu ba da bayanai da kuma dillalan makamai ga ‘yan bindiga.

"Gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen rusa duk wani gida da aka bayar haya ga masu aikata laifi."

KU KARANTA: Idan Ba Za Ka Iya Ba Ka Ba da Wuri, ECWA Ta Bukaci Buhari Ya Yi Murabus

A wani labarin, Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi kira ga mazauna yankin da su kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga amma su tabbatar ba su karya doka ba, Channels Tv ta ruwaito.

Yankin Arewa-maso-Yamma na daya daga cikin yankunan da 'yan ta'adda suka fi addabar al'umma.

"Mutane kada su dauki doka a hannunsu ba, amma ya kamata su dauki matakan doka yadda ya kamata don kare al'ummominsu yayin da wasu gungun 'yan ta'adda suka afka musu," in jiwata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Ibrahim Magaji Dosara ya fitar a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel