Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Wani Dalibin Jami'ar Greenfield ta Kaduna da Aka Sace

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Wani Dalibin Jami'ar Greenfield ta Kaduna da Aka Sace

Daya daga cikin daliban da aka sace a jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna ya kubuta daga hannun 'yan bindiga.

Duk da cewa har yanzu ‘yan sanda da hukumomin gwamnati ba su tabbatar da hakan ba, mahaifiyar daliban, Lauritta Attahiru ta tabbatar da sakin danta ga gidan Talabijin na Channels, a ranar Talata.

Amma duk da haka ta ki bayar da cikakken bayani game da yadda aka saki dan nata kuma an biya fansa ko a'a.

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Wani Dalibin Jami'ar Greenfield ta Kaduna da Aka Sace
Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Wani Dalibin Jami'ar Greenfield ta Kaduna da Aka Sace Hoto: thenationonline.net
Asali: UGC

Wasu daga cikin iyayen sun fada cewa an sako dalibin ne a ranar Asabar bayan mahaifiyarsa, wacce matar wani hafsan soja ne mai ritaya daga jihar Filato ta tattauna kuma ta biya ‘yan bindigan kudin fansa a asirce kafin su sako danta.

Tun da farko iyayen sun sanar da cewa 'yan bindigan sun tattauna da su daban-daban, inda suka nemi kowannensu ya biya sama da Naira miliyan 20, kafin daga bisani su nemi mafi karancin Naira miliyan 100 da babura goma a ranar Litinin, 3 ga Mayu.

Iyayen sun yi kira ga gwamnati da 'yan Najeriya da su kawo musu dauki domin a ceto 'ya'yansu da ransu daga hannun wadanda suka sace su.

Tare da sakin dalibin, makomar sauran daliban 16 har yanzu tana nan a cikin halin ko in kula yayin da 'yan bindigan suka yi barazanar kashe su idan iyayensu da gwamnati suka kasa biyan kudin fansa na Naira miliyan 100 da kuma samar da sabbin babura goma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.