Ku Ƙara mana Lokaci kar ku kashe 'yayan mu, Iyayen Ɗalibai sun Roƙi yan Bindiga
- Ƙungiyar iyaye malamai ta ƙasa NAPTAN ta yi kira ga yan bindigar da suka sace ɗaliban jami'ar Greenfield Kaduna da su ƙara bada lokaci domin tattaunawa
- Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Haruna Ɗanjuma ne ya bayyana haka, yace bai kamata yan bindigan su rinka kashe waɗanda babu ruwansu ba
- Ɗanjuma ya kuma kira yi yan bindigar da suji tsoron Allah su daina abubuwan da suke yi domin ba dai-dai bane
Ƙungiyar iyaye malamai ta ƙasa NAPTAN, ta yi kira ga yan bindigan da suka sace wasu ɗalibai a jami'ar Greenfield Kaduna da su ƙara lokaci domin a cigaba da tattaunawa wajen nemo maslaha.
KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani
Shugaban ƙungiyar NAPTAN, Alhaji Haruna Danjuma, shine ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da jaridar Vanguard ranar Talata.
Shugaban ya kuma roƙi yan bindigar da kada su bari rashin jituwar dake tsakaninsu da gwamnatin Kaduna yasa su ɗauki matakin da bai dace ba.
Ɗanjuma ya kuma yi kira ga yan bindigar da suji tsoron Allah Kada su kashe ɗaliban da babu ruwansu.
Yayi wannan jawabi ne domin martani ga barazanar da yan bindigar sukayi cewa, matuƙar ba'a biya su 100 miliyan kuɗin fansa ba kafin ranar Talata, to zasu kashe ragowar ɗalibai 17 dake hannunsu.
Ɗanjuma yace:
"A tunani na, ya kamata gwamnatin Kaduna ta sake yin nazari a kan matsayarta, Ina ganin tattaunawar neman maslaha da yan bindiga bawai yana nuna cewa dole gwamnati ta biya su kuɗi bane, Ina ganin tattaunawar bata wuce gwamnati tasan dalilinsu na aikata wannan aikin ba da kuma su waye suka aikata."
"Mu ɗauka cewa yan bindigar sun bukaci a biya su wasu kuɗi, idan gwamnati ba zata biya ba to ta bari iyayen ɗaliban su haɗa kuɗin su biya. Naji labarin iyayen ɗaliban sun haɗa 50 miliyan sun baiwa yan bindigar duk da ban da tabbaci akan hakan."
KARANTA ANAN: Gwamnatin Kogi Tayi Cikakken Bayani Kan Kisan da Yan Bindiga Suka Yiwa Kwamishinanta
"Amma bai kamata gwamnati ta tsaya hakanan bata yin komai ba, Shin akwai ƴaƴan jami'an gwamnati a cikin waɗanda aka sace ɗin? Nasan amsar ba zata wuce a'a ba."
"Ina roƙon yan bindigar nan a madadin sauran iyayen yaran da su taimaka su barsu a raye. Ya kamata su ji tsoron Allah, su daina zubar da jinin wandanda ba ruwansu." inji shi.
Idan zaku iya tunawa a ranar 20 ga watan Afrilu, wasu yan bindiga suka sace ɗalibai a jami'ar Greenfield Kaduna, bayan wasu yan kwanaki kuma suka kashe biyar daga cikinsu.
A ranar Litinin kuma, yan bindigar sun yi barazanar sheƙe ragowar 17 dake hannunsu matuƙar ba'a biyasu 100 miliyan da kuma mashina 10 a matsayin fansa ba kafin yau Talata.
A wani labarin kuma Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 17 a Wani Sabon Hari a Jihar Benuwai
Akalla mutane 17 ne suka rasa rayuwarsu a wasu jerin hare- hare da yan bindiga suka kai wasu ƙauyuka a jihar Benuwai.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan ɗauke da muggan makamai sun kai harin ne ranar Lahadi da yamma da kuma Litinin da safe.
Asali: Legit.ng