Labaran garkuwa da mutane
Zamfara - Biyu daga cikin malamai da kuma wani ɗalibi ɗaya da yan bindiga suka sace a kwalejin noma dake Bakura, jihar Zamfara sun tsero sun koma makaranta.
Niger - Jami'an yan sanda a jihar Neja sun samu nasarar kubutar da shugaban jam'iyyar APC shiyyar C a Neja, wanda yan bindiga suka sace a kan hanyar zuwa gona.
Rundunar NDLEA ta cafke wasu 'yan bindiga da ke dauke da muggan makamai a hanyarsu ta zuwa wani gari watakila domin gudanar mummunan aikinsu ta fashi da makami.
Taraba - Wasu mazauna ƙauye a jihar Taraba sun fusata, inda suka yi gaba-da-gaba da yan bindigan da suka kawo musu hari domin satar mutane, sun kashe ɗaya.
Wasu yan fashi sun bi dare sun harbi tsohon kansila sannan suka yi awon gaba da matarsa da kuma ɗan jaririnta da bai wuce watanni 7 da zuwa duniya ba a Zamfara.
Yan fashin daji sun tare motar yan bikin aure inda suka tasa baki ɗaya waɗanda suke cikin motar zuwa cikin daji, amma jami'an tsaro sun ɗauki matakin gaggawa.
Labarin dake shigowa yanzun daga jihar Neja na nuna cewa wasu masu garkuwa sun yi awon gaba da shugaban jam'iyyar APC na shiyyar C, Aminu Bobi, da yammacin yau.
Gwamnatin Buhari ta yi bayanin dalilin da yasa ba zata amince ta zauna zaman tattaunawa da 'yan bindiga masu sace dalibai ba. Ta ce ba za ta amince da hakan ba.
Wani matashi mai shekaru 16 ya shiga hannun 'yan sanda a jihar Oyo yayin da ya kitsa sace wani mutum da sunan zai sayar masa da wasu shanun da babu su a wurinsa
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari