Tinubu Ya Yi Martani da Janar Rabe Abubakar Ya Rasu a hannun 'Yan Bindiga

Tinubu Ya Yi Martani da Janar Rabe Abubakar Ya Rasu a hannun 'Yan Bindiga

  • Shugaba Bola Tinubu ya jajanta wa iyalan Manjo Janar Rabe Abubakar bayan rasuwarsa a hannun masu garkuwa da mutane a Katsina
  • Fadar shugaban kasa ta ce gwamnati ba za ta taba sakin ‘yan ta’adda da ake tsare da su domin biyan bukatun masu garkuwa ba
  • Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana rasuwar tsohon daraktan yada labaranta a matsayin babban rashi ga kasa baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhini kan rasuwar tsohon Manjo Janar, Rabe Abubakar wanda ya mutu a hannun masu garkuwa da mutane a Katsina.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, Tinubu ya bayyana rasuwar a matsayin abin takaici da girgiza kasa.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami ya yi zargin akwai lauje cikin nadi kan mutuwar Sani Abacha

Mutuwar Janar Rabe Abubakar a hannun 'yan bindiga ta girgiza Tinubu
Shugaba Bola Tinubu (hagu) da Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) da ya rasu a hannun 'yan bindiga. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya jajanta wa iyalan Janar Rabe

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na X a ranar 13 ga Yunin 2025.

Sanarwar ta ce marigayin ya yi ritaya daga aikin soja bayan doguwar hidima ga kasa, kuma yana hanyarsa ta zuwa garinsu ne lokacin da ‘yan bindiga suka sace shi.

Shugaban kasar ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, musamman matarsa wadda har yanzu take a hannun masu garkuwar.

Haka kuma Tinubu ya jajanta wa gwamnatin jihar Katsina da rundunar sojojin Najeriya bisa wannan babban rashi.

Shugaba Tinubu ya gargadi 'yan bindiga

Tinubu ya ce duk da abin takaicin da ya faru, gwamnati ba za ta taba amincewa da bukatar masu garkuwa ta sakin ‘yan ta’adda da jami’an tsaro ke tsare da su ba.

Ya sake jaddada gargadin da ya yi a ranar Dimokuradiyya ga ‘yan bindiga da masu daukar nauyin ta’addanci da su mika wuya ko su fuskanci karfin gwamnati.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi maganar mutuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'yan Bindiga

“Ba za a ci gaba da bude kofar afuwa har abada ba. Ba za a nuna jin kai ga masu zubar da jinin ‘yan Najeriya ba,” in ji Tinubu.

Hedikwarar tsaro ta yi jimamin rasuwar Janar din

Hedikwatar tsaron Najeriya ta kuma tabbatar da rasuwar tsohon daraktan yada labaran tsaro na rundunar soji, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Hedikwatar tsaro ta yi alhinin rasuwar Janar Rabe Abubakar.
Janar Rabe Abubakar, tsohon babban sojan Najeriya da ya mutu a hannun 'yan bindiga. Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

A wata sanarwa da Daraktan yada labaran tsaro, Samaila Uba, ya fitar, rundunar sojin Najeriya ta bayyana alhini kan mutuwar marigayin a hannun masu garkuwa.

“Hedikwatar tsaro na bakin cikin sanar da rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasa ransa a lokacin da yake hannun masu garkuwa bayan sace shi,” in ji sanarwar.

Hedikwatar ta mika ta’aziyya ga iyalan marigayin da abokan aikinsa da daukacin ‘yan Najeriya bisa wannan babban rashi.

Tinubu ya ce rasuwar Janar Rabe Abubakar ya kamata ta kara karfafa yaki da ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya a Najeriya.

Janar Rabe ya mutu a hannun 'yan bindiga

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), wanda yan bindiga suka yi garkuwa da shi tare da matarsa a jihar Katsina, ya rasu

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar, an ji halin da matarsa ke ciki a hannun 'yan bindiga

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwar tsohon Janar Rabe Abubakar, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga.

A cewar Gwamnatin Katsina, tsohon janar din ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka hada da ciwon sukari da kuma hawan jini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com