Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri

Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri

  • Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, ya bayyana cewa shugabannin fulani ba su da hannu a sace ɗaliban FGC Yauri
  • Gwamnan yace waɗanda suka sace ɗaliban fulani ne da suka fi zama a daji yan wata tawaga mai suna renegade
  • Bagudu yace gwamnatinsa ba zata bari haka ya cigaba da faruwa ba, kuma ya kamata kowane mutum ya shirya

Shugabannin Fulani na jihar Kebbi sun musanta zargin cewa suna da hannu a sace ɗaliban makarantar sakandiren gwamnatin tarayya FGC Yauri, kamar yadda premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wasu Fusatattun Ɗalibai Sun Yi Fata-Fata da Cibiyar Zana Jarabawar JAMB CBT

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, shine ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Buhari.

Shugaba Buhari Tare da gwamnan Kebbi
Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri Hoto: kebbistate.gov.ng
Asali: UGC

Mr. Bagudu ya je har fadar shugaban ƙasa ,inda suka zanta da shugaba Buhari a kan lamarin.

Yace mafi yawancin ɓarayin yan fulani ne, kuma ana samun irin su cikin daji saboda haka yanayin rayuwarsu take.

Gwamnan ya bayyana cewa shugabannin fulani a jihar Kebbi sun fito sun yi Allah wadai da satar ɗaliban, wanda wata ƙungiya da ake kira 'Renegade' suka yi.

KARANTA ANAN: Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamna Atiku Bagudu Kan Ɗaliban FGC da Aka Sace

Gwamna Bagudu yace gwamnatinsa ba zata amince da irin wannan harin ba

Mr. Bagudu ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba zata amince irin haka ta cigaba da faruwa ba a jihar.

Yace: "Na bayyana a fili cewa ba zamu amince da irin wannan ba, kuma ba zamu bari haka ta cigaba da faruwa ba da izinin Allah."

"Kowa ya shirya zamu fuskanci marasa son zaman lafiya da yan ta'addan da suka addabi yankin mu. Ba aikin jami'an tsaro bane su kaɗai, ya kamata mu taimaka musu, kuma mu shirya."

A wani labarin kuma Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya ƙara jaddada maganarsa kan cewa duk wanda ya ɗauki makami ya yaƙi Najeriya zai fuskanci hukunci

Shugaban yace matasa na da rawar da zasu taka domin gina goben su da kuma ƙasar su, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262