Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin artabu da 'yan sanda

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin artabu da 'yan sanda

  • Rahotanni sun ce rundunar 'yan sanda sun dakile wani harin 'yan bindiga a wani yankin jihar Benue
  • An hallaka 'yan bindiga 14 yayin mummunan musayar wuta da ya faru tsakaninsu da 'yan sanda
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta kuma yi kira ga ba da bayanai masu amfani

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Benue ta tabbatar da cewa 'yan bindiga 14 sun mutu a yayin musayar wuta bayan wani yunkurin kai hari a wani ofishin 'yan sanda a garin Katsina-Ala, jihar Benue da safiyar Lahadi, The Nation ta ruwaito.

Mai magana da yawun ‘yan sanda DSP Kate Anene, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce a ranar Asabar, an kama wasu da ake zargin 'yan bindiga ne kuma an tsare su a ofishin ‘yan sanda da ke Katsina-Ala domin gudanar da bincike.

KU KARANTA: Kasar Isra'ila ta tsorata bayan mai tsattauran ra'ayi a kasar Iran ya lashe zabe

'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Hallaka 14
'Yan Bindiga Dauke da Muggan Makamai | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Amma ta ce a safiyar ranar Lahadi, da misalin karfe 1 na dare, wasu ‘yan bindiga, wadanda yawansu ya kai 50, sun kai wani mummunan hari a ofishin 'yan sanda a kokarin su na kubutar da wadanda ake zargin dake tsare.

Mai magana da yawun 'yan sandan ta ce jami'an sashin, wadanda tuni sun kasance cikin shirin ko ta kwana, sun yi artabu da 'yan bindigan tare da bindige 14 daga cikinsu a yayin musayar wuta yayin da wasu suka tsere da raunin harsasai da dama.

A rahoton Daily Nigerian, 'yan sanda sun shawarci jama'ar Katsina-Ala da su kwantar da hankulansu tare da bai wa 'yan sanda bayanai masu amfani.

KU KARANTA: Ba zai yiwa ba: Shugaba Buhari ya ce ba ga kowane dan siyasa zai mika mulki ba

Yadda 'Yan Bindiga Suka Yi Amfani da Motar Mahaifin Dalibi Wajen Sace Daliban Kebbi

A wani labarin, Rahotanni da Legit.ng Hausa ta samo sun bayyana cewa, 'yan bindigan da suka sace dalibai a jihar Kebbi sun yi amfani da motar wani mahaifin dalibi ne wajen sace daliban.

Idan baku manta ba, wasu mahara sun kai hari kwalejin gwamnatin tarayya dake garin Yauri a jihar Kebbi a ranar Alhamis kuma sun yi awon gaba da dalibai da ma’aikata, jaridar Guardian ta ruwaito.

Wani malami da bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa Daily Trust cewa kafin harin, sun samu labarin wani shiri na mamaye garin na Birnin Yauri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.